“Baka Ji Kunya Ba?” Matashiya Ta Caccaki Saurayinta Kan Tura Mata N70k Maimakon N400k

“Baka Ji Kunya Ba?” Matashiya Ta Caccaki Saurayinta Kan Tura Mata N70k Maimakon N400k

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yi barazanar rabuwa da saurayinta saboda ya aika mata N70,000 maimakon N400,000
  • A wani faifan murya da ya bayyana, budurwar ta umurci saurayin da ya aike mata N400,000 ko su rabu
  • Hirarsu ta Whatsapp ya haifar da martani da dama daga jama'a wadanda ke ganin budurwar a matsayin mai idon cin naira

Wani faifan murya da ya yadu ya fallasa hirar da ya gudana tsakanin wasu masoya da suka samu matsala saboda kudi.

Budurwar ta yi barazanar rabuwa da saurayinta saboda ya aike mata 70k bayan ta sanar da shi shirye-shiryenta na komawa makaranta.

Matashiya da saurayi
“Baka Ji Kunya Ba?” Matashiya Ta Caccaki Saurayinta Kan Tura Mata N70k Maimakon N400k Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

A faifan muryar wanda @instablog9ja ta wallafa, ta bukaci saurayinta ya tura mata N400,000, ko kuma ta rabu da shi.

Kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

“Kanwata Ce Ta Jini”: Matashi Ya Zauce Bayan Ya Hadu Da Mahaifin Budurwar Da Ya Yi Wa Ciki a Karo Na Farko

"Me yasa ka aika mani 70k, irin ban fahimta ba na fada maka zan koma makaranta amma abun da za ka iya tura mun shine 70k? Me zan yi da naira dubu 70, sa'o'inka na turawa yan matansu dubu 700, 800 ko ma 900k amma kai kana nan kana tura mani naira dubu 70.
"Wayyo Allah wato ko kunyar kanka baka ji ba? Ka saurare ni idan za ka iya tura mun 500 bari ma dai na yi aiki da hankali, idan ba za ka iya tura mun 400k ba ka sa a ranka soyayyar nan ta kare, ba zan iya ci gaba da shi ba."

Jama'a sun yi martani

@pharoahshound_tattoos_ ta ce:

"Ya kamata bankuna su kara wajen mayar da kudi a manhajarsu."

@deacondammy ta yi martani:

"Ta yi kamar namiji ne yake tilasta kansa yin muryar mata."

@sleek_lion ta ce:

"Me yasa baki tambayi mahaifinki kudi ba? Hajiya za ki dawo da 70k dinnan."

Kara karanta wannan

Kujerar Kakaki: Ado Doguwa Ya Ce Mata 4 Da 'Ya'ya 28 Yake Dashi, Zai Iya Ji da Majalisa

@_prom.queen ta ce:

"Kin ma ga 70k, a ina kuke haduwa da irin wadannan mazajen masu kirki."

Amarya ta koka bayan ruwan sama ya tarwatsa taron bikinta

A wani labarin, wata amarya ta koka a ranar aurenta bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya barke ana tsaka da shirye-shiryen bikinta.

Masu kawata wajen sun kammala kenan sai ga ruwan sama ya sauka lamarin da ya kawo cikas ga taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel