"Na Wanke Shi Tas", Dirarriyar Budurwa Ta Yaudari Mahaifinta a Matsayin Budurwarsa, Ya Tura Mata Kudade

"Na Wanke Shi Tas", Dirarriyar Budurwa Ta Yaudari Mahaifinta a Matsayin Budurwarsa, Ya Tura Mata Kudade

  • Wata budurwa ta garzaya yanar gizo domin bayar da labarin yadda ta karɓi kuɗi a hannun mahaifinta wanda ya ke neman masoyiya
  • A wani labari da ta sanya a manhajar Twitter, ranar 29 ga watan Afirilu, budurwar tace ta yaudari mahaifinta a Tinder inda ya tura mata kuɗi
  • Labarin na ta ya ɗauki hankali sosai a Twitter, inda mutane suka yi ta muhawara akan sa, da yawa sun ce ƙarya ta shararo

Wani magidanci ya turawa ɗiyar sa kuɗi a tunanin cewa itace masoyiyar da ya ke nema.

Ɗiyar magidancin itace ta garzaya yanar gizo domin bayar da labarin a shafin ta na Twitter mai suna @NanaWanido.

A cewar ta lamarin ya auku ne a manhajar Tinder, wata manhaja inda masoya ke haɗuwa, inda tace ta je da sunan bogi wajen mahaifin na ta.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana

Budurwa ta yaudari mahaifinta a yanar gizo
Budurwar tace ta yaudari mahaifinta ya tura mata kudi (hotunan amfani kawai aka yi da su domin nuni) Hoto: GettyImages/PeopleImages, Bloomberg da Momo Productions
Asali: Getty Images

Budurwar ta bayyana cewa ta garzaya manhajar ne inda ta haɗu da mahaifin ta, wanda ya je neman masoyiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta:

"Na je da sunan bogi ga mahaifina a Tinder. Mutuminka kawai ya turo min kuɗi."

Mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi akan labarin na ta. Yayin da wasu suka yarda da ita, da yawa sun ce labarin na ta bai faru ba, ƙirƙirar sa kawai ta yi.

Labarin na ta ya yaɗu sosai

Ta sanya labarin ne a ranar 29 ga watan Afirilun 2023, amma ya zuwa ranar 3 ga watan Mayun 2023, har mutum dubu 634k sun karanta sannan mutum 351 sun danna masa 'like'.

Ga kaɗan daga cikin ra'ayoyin da aka bayyana:

@mmase2mola ya rubuta:

"Na kasa yarda saboda hakan na nufin kin yi ta nema har sai da kika gano shi kenan, wanda hakan akwai alamar tambaya, saboda me zai sanya ya ɗora hoton sa idan ya tsufa kuma yana da aure. Sannan me kika gaya masa da haka kawai ya turo mi ki kuɗi bai sanki ba."

Kara karanta wannan

Halin da Wasu Ɗaliban Najeriya Suka Shiga Bayan Motar da Ta Kwaso Su Daga Sudan Ta Kama da Wuta

@Khathu_M_ ta rubuta:

"Ɗaya daga cikin abinda ba su faru ba, amma dole sai mun nemi suna."

@hazel_phali ya rubuta:

"Kina nufin caskalewa kike da mahaifin ki?"

@nobengunii ya rubuta:

"Ki daure ki ga likitan ƙwaƙwalwa."

@realnickjgood ta rubuta:

"A bayyane ya ke ku duka ba ku taɓa amfani da Tinder ba, ba a neman sunan wani kamar yadda ake yi a Facebook."

Masoya Sun Yi Fice a Intanet Bayan Saurayi Ya Gwangwaje Sahibarsa Da Kyautar Mota

Wasu masoya biyu sun bar mutane baki buɗe bayan saurayi ya gwangwaje rabin ran sa da kyautar dalleliyar mota.

Bidiyon masoyan biyu ba ƙaramin sanya mutane farin ciki da annushuwa marar misaltuwa ya yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel