Komai Lokaci Ne: Wata Mata Data Kashe ₦6,233,688 Don Cin Jarabawar Koyar Mota Sau 960 Tayi Nasara Daga Karshe

Komai Lokaci Ne: Wata Mata Data Kashe ₦6,233,688 Don Cin Jarabawar Koyar Mota Sau 960 Tayi Nasara Daga Karshe

  • Cha Sa-soon daga Korea ta Kudu tayi ta ƙoƙarin ganin ta samu lasisin tuƙi, amma tana gaza samun nasara
  • Bayan kashe Fam ɗin Ingila £11,000 (₦6,233,688), daga ƙarshe dai ta samu nasarar samun lasisin
  • Hakan na zuwa ne a lokacin data jure, ta dage ta hanyar kome kome wajen jarrabawa tare da faɗuwa da sake jarabawa har sau 960

Korea Ta Kudu - Sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba'a je ba, inji kunkuru ga kare.

Wata mata data kashe kuɗi kimanin miliyan ₦6,233,688 domin samun lasisin tuƙi ta samu nasarar samun lasisin bayan shafe lokaci mai tsawo wajen jarabawa.

Matar mai naci, ta shafe kimanin shekaru 15 ba abin da take sai ƙokarin neman wannan lasisi.

Korea
Komai Lokaci Ne: Wata Mata Data Kashe ₦6,233,688 Don Cin Jarabawar Koyar Mota Sau 960 Tayi Nasara Daga Karshe Hoto: dailymail.co.uk
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Labarin matar yaja hankalin duniya ne biyo bayan karaɗe kafar sadarwar nan ta Reddit, akan yadda ta jajirce wajen samun burin zuciyar ta wato lasisi.

Matar ta yi ƙoƙarin cin jarabawar samun lasisin ta nafarko ne a watan Afrilun shekarar 2005, amma bata samu nasara.

Duk da haka, matar ƴar Korea ta Kudu bata gajiya ba, haka tayi ta gwadawa tana faɗuwa.

Sai da ta dinga ɗaukar jarabawar kullum, wato kwana biyar a sati na tsawon shekaru biyar.

Koda ta fahimci cewar abin nayi ne, sai ta rage wannan adadi, zuwa zana jarabawar sau biyu a sati, wanda Allah cikin ikon sa, sai a ƙoƙarin ta na 850 ta samu nasarar cin jarabawar.

Data samu nasarar cin jarabawar, sai ta ɗaura belt din ta na sitiyarin mota, wanda shima ta haɗu da ƙalubale babba wajen jarabawar tuƙi ta zahiri.

Sai da Cha Sa-Soon tayi jarabawa a wannan mataki har sau goma, kafin ta dace, wanda ya kawo adadin jarabawowin data zana zuwa 960 na daga jarabawar rubutu da kuma jarabawa ta zahiri.

Kara karanta wannan

Jihar Gombe Da Sauran Jihohin Da Ake Kasuwanci a Saukake, Sabon Rahoto Ya Bayyana

Kudin data kashe ya kai €12,500 wato fam (£11,000) daidai da kuɗin Najeriya ₦6,233,688.

Abin ban sha'awa shine, duk da tsadar kudin da matar ta kashe, amma hakan baisa ta gaji ba, haka tayi ta ƙoƙari har tasamu nasara.

Duk don saboda ta samu damar tuƙa motar da take saida kayan gwari zuwa kasuwanni.

Shi kansa malamin da yake koya mata motar, yace lokacin data sami nasara, ba ƙaramin dad'i suka ji ba, saboda ta zame musu kamar wani nauyi da suke so su yakace.

A cewar malamin dake koyar wa matar mota a makarantar Jeonbukta ta koyon tuƙi:

"Muna jin ta samu nasarar samun lasisin ta bayan dogon ƙokartawa, dukkan mu sai da muka fita waje muna murna tare da rungumar ta, har sai da muka bata furanni."

Ya ƙara da cewa:

"Ji mukayi kamar an sauke mana nauyin dala da gwauron dutse daga kafaɗar mu. Bamu da ƙwarin gwuiwar ce mata ta haƙura, saboda naci. Kullum sai tazo".

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya Sun Halaka Babban Ɗan Ta'adda da Wasu Mayaƙa Sama da 40 a Arewa

Labarin na Cha Sa-soon ya karaɗe manya manyan kafafen yaɗa labarai na duniya, wanda hakan yasa ta zama shahararriya a ƙasar ta.

Jaridar Dailymail ta Burtaniya ta ruwaito yadda babban kamfanin haɗa motocin nan na Hyundai na Korea ta Kudu, sai daya bata mota sabuwa fil mai darajar €13,000 (£11,640) samfurin Hyundai.

Biki Ya Tarwatse Yayin da Amarya Ta Gano Ango Ashe Yana Da 'ƳaƳa 7

Boye sirri a tsakanin ma'aurata na cigaba da zama matsala a alaƙa. Wata amarya taga abin mamaki, sanda ta ankare da wani sirri na angon dabai faɗa mata ba.

Matar ta gano cewar angon nata yana da ƴaƴa bakwai rigis. Wanda hakan yasa tace ai kam lamarin nan bada ita ba, gobarar titi a Jos. Tuni ta hargitsa taro tace baza'a ayi lamarin nan da ita ba.

Jaridar legit.ng ta ruwaito yadda wani hoto mai motsi na wajen bikin da yadda yayi fata fata ya sanya mutane suka shiga mamaki da kuma canja ra'ayin da ya jawo kace nace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel