Taron Biki Ya Tarwatse a Benin Bayan Amarya Ta Gano Ango Yana Da 'Ya'Ya 7

Taron Biki Ya Tarwatse a Benin Bayan Amarya Ta Gano Ango Yana Da 'Ya'Ya 7

  • Wani bikin aure ya tarwatse a ranar ɗaurin aure bayan amarya ta gano wani ɓoyayyen sirrin angon
  • Cikin abinda ya zama mai matuƙar mamaki ga amaryar, ta gano cewa angon yana da mata har da ƴaƴa bakwai
  • Bidiyon yadda wajen bikin yayi kaca-kaca ya sanya mutane masu amfani da yanar gizo musayar ra'ayi

An tarwatse daga wajen wani taron biki bayan an gano cewa angon yana da aure har da ƴaƴa bakwai.

Wani shaidar gani da ido wanda ya kawo rahoton a TikTok ya nuna wurin taron bikin, wanda mutane suka watse daga wajen.

Bikin Aure
Tirkashi: Taron Biki Ya Tarwatse a Benin Bayan Amarya Ta Gano Ango Yana Da 'Ya'Ya 7 Hoto: TikTok/Samuganlisa123
Asali: UGC

Wasu mutane na maƙale a wurare daban-daban yayin da akayi fata-fata da kayan kwalliyar da aka yiwa wurin taron bikin.

A cewar ganau ba jiyau ba, lamarin dai ya auku ne a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Farmaki Wasu Kauyuka a Jihar Bauchi, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah Masu Yawa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganau ɗin wanda namiji ne ya ɗora alhaki aukuwar hakan akan amaryar inda yace ba tayi bincike mai kyau yadda yakamata akan angon.

Mutane sun yi tsokaci

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su bayan sun yi arba da bidiyon, inda da yawa daga ciki suka fi damuwa kan kayan lashe-lashen da aka kawo a wajen bikin.

Ga kaɗan daga ciki:

Yung Christo ya rubuta:

"Akwai ƙarancin mazan aure amma har yanzu samari neman ƴanmata suke basu samu ba."

Lush ta rubuta:

"Wannan katafaren biki haka bayan sun san cewa basu shuka gaskiya ba."

nickyberrymo ya rubuta:

"Ku dai na faɗin hakan. Idan fa angon bai gaya mata cewa yana da aure ba fa? Ba laifin ta bane."

Wiseman studio ya rubuta:

"Ta yaya wannan zai zama matsala? Damuwa ta itace ana murnar ranar mahaifiya ranar Lahadi ni kuma ina gida ina kuka saboda mahaifiyata tana kwance a kabari. Wannan yafi min ciwo."

Kara karanta wannan

Maciji Ya Kashe Hatsabibin Babban Kwamandan ISWAP A Dajin Sambisa

Dekay ya rubuta:

"Yanzu da wane ido zai kalli matar sa? Kafin nan dai ya fara biyan kuɗin haya, DJ da kuɗin kwalliya tukunna. Irin wannan ba baƙon abu bane a Benin."

Bayan Rabuwa Da Tsohon Saurayinta, Budurwa Ta Koma Soyayya Da Mahaifin Sa

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta kwancewa tsohon saurayin zani a kasuwa, ta koma soyayya da mahaifin sa.

Budurwar ta yi hakan ne bayan sun rabu da tsohon saurayin na ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel