Sojoji Sun Kashe Kwamandan Yan Ta'adda da Wasu Mayaka 41 a Borno

Sojoji Sun Kashe Kwamandan Yan Ta'adda da Wasu Mayaka 41 a Borno

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe mayakan ISWAP 41 a jihar Borno da ke arewa maso gabas
  • Zakazola Makama, yace wata majiyar soji ta faɗa masa cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da kwamandan yan ta'ddan
  • Bayan haka wasu mayakan ISWAP sun kwashi kashinsu a hannun Sojoji yayin da suka kai farmaki kauyen Konduga

Borno - Rundunar Operation Haɗin kai da haɗin guiwar dakarun CJTF, sun aika mayakan kungiyar ISWAP 41 barzahu a ƙaramar hukumar Dikwa, jihar Borno.

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce Abu Zahra, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ISWAP na cikin waɗanda suka mutu.

Sojojin Najeriya
Sojoji Sun Kashe Kwamandan Yan Ta'adda da Wasu Mayaka 41 a Borno Hoto: Army
Asali: Twitter

A shafinsa na Tuwita, Makama ya ce rundunar sojin ta kai wannan samame karkashin jagorancin Shaibu Waidi, shugaban runduna ta 7 domin ɗaukar fansar harin da ISWAP ta kai ƙauyen Mukdolo.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Manyan Jiga-Jiganta a Jihohi 5, Ta Ɗauki Mataki Kan Wani Gwamnan Arewa

"Wani kwamandan 'yan ta'adda (Amir Jaysh) Abu Mohammed, tare da wasu tsirarun mayaƙa sun sha da kyar sanadin luguden wutan Sojoji."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ruwan wutan sojin ya sa suka gudu suka bar kadarorinsu da maƙudan miliyoyin naira a cikin gidajensu, kuma sojojin ba su yi wata-wata ba suka lalata su," Makama ya wallafa.

Bugu da kari, Dakarun sojin sun kwato Motar yaƙi, babura da sauran mayan makaman Sojoji daga hannun miyagun 'yan ta'addan.

Haka nan an tattaro cewa mutane sun nuna farin cikinsu a Konduga, jihar Borno ranar Asabar bayan dakarun Bataliya ta 222 sun sha ƙarfin mayakan ISWAP.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun farmaki sansanin Sojin da ke ba da kariya ga ƙauyen da misalin karfe 6:45 na ranar Asabar.

Nan take Jami'an sojin suka maida martani, aka yi musayar wuta mai zafi, daga ƙarshe 'yan ta'adda da yawa suka zarce lahira, wasu kuma suka ari na kare.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro Sama da 50 a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Coci, Sun sace Matarsa a Kaduna

A wani labarin kuma Yan bindiga sun halaka malamin Coci kana suka yi garkuwa da matarsa a karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Shugaban CAN na Kaduna, Rabaran Hayab, ya ce bayan haka yan ta'addan sun sako akalla mutane 100 da suka sace a garuruwa daban-daban na jihar.

Ya ce har yanzun akwai wani Malamin coci dake hannun masu garkuwa da mutane tun bayan gama zaɓen shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel