"Ba Lafiya": Dirama A Yayin Da Mawaki Portable Ya Iso Wurin Wasa A Cikin Akwatin Gawa, Bidiyon Ya Bazu

"Ba Lafiya": Dirama A Yayin Da Mawaki Portable Ya Iso Wurin Wasa A Cikin Akwatin Gawa, Bidiyon Ya Bazu

  • Mawakin Najeriya mai tashe, Portable Zazu ya yi wasa a New African Shrine a ranar 28 ga watan Disamba kuma ya bawa masoyansa mamaki
  • Wani abin da ya dauki hankulan mutane sosai shine lokacin da aka kawo Zazu mimbarin waka cikin akwatin gawa ya fito yana kwalisa
  • Bidiyon ya janyo mutane suna ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi inda wasu suka nuna rashin gamsuwarsu da abin da ya yi

Mawakin Najeriya mai tashe Portable Zazu, wanda aka sani da yawan yin abubuwa da ba a saba gani ba ya sake aikata wani abu da ya dauki hankalin mutane a wasan da ya yi a New African Shrine a daren ranar Laraba 28 ga watan Disamba.

Wani bidiyo daga taron ya nuna lokacin da Portable ya shiga akwatin gawa kuma aka dauke shi zuwa inda zai fara waka sannan ya fito ya fara waka.

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude

Portable
"Ba Lafiya": Dirama A Yayin Da Mawaki Portable Ya Iso Wurin Wasa A Cikin Akwatin Gawa, Bidiyon Ya Bazu. Hoto: Credit: @portablebaeby
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga bidiyon a kasa:

Baya ga Portable, wasu mawaka masu tasowa suma sun yi wasa a wurin taron.

Ga bidiyon wasu daga cikinsu a kasa.

Portable ya gwangwaje rawansa a bidiyon.

Candy Bleaks shima ya yi wasa wurin bikin.

Yan Najeriya sun yi martani a yayin da Portable ya iso wurin waka cikin akwatin gawa.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da masu amfani da intanet suka yi na nuna rashin amincewarsu da abin da mawakin ya yi.

Ga dai abubuwan da wasu cikinsu suka ce:

churchill_777:

"Kafin Olamide ya sake daukan wani mawaki, ya kamata su kawo rahoton likita."

churchill_777:

"Wanda ya gabatarwa mana Portable, ya kamata ya nemi afuwar yan Najeriya."

blesseddbarber_:

"Wannan ya fi karfin taro ko baku sani bane... amma kuna zaton salon taro ne kawai ko... wadannan suna kokarin ceto rayuwarsu ne suna wasu surkulle saboda kada wani ya iya isar masa... wannan ya fi karfin abin da aka saba gani. Ku farka."

Kara karanta wannan

Juya Nake So Wacce Za Mu Sha Soyayya, Tsoho Ya Roki Fasto Ya Aura Masa Mata Ta 5

vv_348:

"A duk yunkurinsa na nuna fasaha, ban yarda da akwatin gawa ba kuma ba za a dauke shi a akwatin gawa ba sai shekarunsa sun kai. Amen."

mide_fwesh:

"Me ya faru da Portable?? Wannan ya yi yawa."

Rundunar yan sanda sun umurci Portable ya kai kansa ofishinta

A baya, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Ogun ya umurci mawaki Portable (Habben Okikiola) ya kai kansa ofishinta maki kusa, idan ba haka ba a kama shi.

Hakan na zuwa ne bayan zargin duka da wani tsohon DJ dinsa, DJ Chicken ya yi a wurin yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel