Rayuwa Juyi-Juyi: Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta Koma UK Da Zama Tare Da Mijinta

Rayuwa Juyi-Juyi: Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta Koma UK Da Zama Tare Da Mijinta

  • Wata matashiya yar Najeriya ta nunawa mutane yadda rayuwarta ta sauya daga mai siyar da tuwo zuwa wacce ke rayuwa a UK
  • Bayan ta nuna yadda ta ke hada tuwonta na rogo sannan a tafi talla, wani bidiyo ya hasko ta tare da mijinta a Turai
  • Mutane da dama sun taya mai tuwon murna yayin da wasu suka roki Allah ya masu irin nata a 2023

Rayuwa ta sauya ta zama sabuwa ga wata matashiya yar Najeriya, @prettyfailuch, wacce ke tallan tuwo a baya. A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, ta nuno yadda take shirya tuwonta na rogo wanda aka fi sani da 'fufu' yayin da take gida Najeriya.

A bidiyo na biyu, an gano ta tana shirya tuwonta a cikin wani roba kafin ta dauka ta tafi yawon talla.

Kara karanta wannan

Himma Ba Ta Ga Rago: Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya Zama Shagon Siyar Da Kaya a Bidiyo

Mata da miji da tukunyan tuwo
Rayuwa Juyi-Juyi: Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta Koma UK Da Zama Tare Da Mijinta Hoto: TikTok/@prettyfailuch
Asali: UGC

Mai tuwo da mijinta sun koma UK da zama

A kusan karshen bidiyon, ta baje fasfot biyu na tafiya waje inda ita da mijinta suke darawa yayin da suke jan jakunkunansu a filin jirgin sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da isan su UK, sun rungume junansu dauke da murmushi a fuskokinsu don nuna tsananin farin cikin da suke ciki na samun damar tsallakawa Turai.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya samu martani fiye da 300 tare da 'likes' fiye da 14,000.

Jama'a sun yi martani

willianfred02 ya ce:

"Ki mutunta mutumin da ke rayuwarki..saboda shi ya sa hakan ya tabbata a gareki...ki dunga tuna daga inda kika fito a kodayaushe."

Sharon ta ce:

"Abun da ya rage yanzu shine na fara siyar da tuwo kamar wannan."

Love ta ce:

"Na tayaki murna yaruwa na hango kaina a chan nima kwanann nan."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwar da Tayi Shekaru 15 a Dubai, Ta Dawo Najeriya Neman Mashinshini

chinny ta ce:

"Na kulla damarar fara siyar da tuwo. Dole sai na isa UK."

SkincarewithMabel ta ce:

"Dan Allah ki yi kokari ki barwa wani kasuwancinki kada ki yi watsi da shi."

ekechukwupascalin ta ce:

"Na taya ki murna ina rokon Allah ya yi mun irin taki ba zan yi watsi da damar ba."

Mara haihuwa nake so, tsoho na ya nemi a aura masa mata ta biyar

A wani labarin, wani dattijo ya gurfana a gaban coci inda ya roki malamin addini da ya roka masa Allah ya bashi matar aure wacce za su karasa rayuwarsu tare.

Tsohon wanda ya ce baya son mai haihuwa ya ce ya auri matansa na farko su biyu amma suka rabu da shi bayan nan ya sake auran wasu biyu suka mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel