Hotuna: Diyar Sanusi Lamido ta Kammala Digiri na 2 a Fannin Shari’a a Landan

Hotuna: Diyar Sanusi Lamido ta Kammala Digiri na 2 a Fannin Shari’a a Landan

  • Hafsat Lamido, daya daga cikin ‘ya’yan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammad Sanusi II, ta kammala digiri ba biyu
  • A hotunan da suka bayyana daga shafin Uwargidan tsohon sarkin, an ga Sanusi II da iyalansa a wurin yayen daliban jami’ar Soas dake Landan
  • Hafsat wacce aka fi sani da Fulani Siddika Sanusi tana da digiri na farko a fannin shari’a kuma ta taba auren Abubakar Umar Kurfi

Landan - Iyalan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi II a halin yanzu suna cikin farin ciki da annashuwa tare da shagali.

Fulani Siddika
Hotuna: Diyar Sanusi Lamido ta Kammala Digiri na 2 a Fannin Shari’a a Landan. Hoto daga @giwar_msII
Asali: Instagram

Hafsat Lamido wacce aka fi sani da Fulani Siddika, daya daga cikin diyoyin tsohon sarkin Kano, ta kammala digirin digir a fannin shari’a daga jami’ar Soas ta Landan.

A ranar Laraba, kyakyawar budurwar ta kammala digirinta na biyu daga jami’ar dake Ingila kuma wasu daga cikin hotunan yayen daliban da yadda ‘yan uwanta suka garzaya taya ta murna sun bayyana.

Idan za a tuna, a watan Yuni da ya gabata ne Mustapha Lamido, ‘dan tsohon sarkin ya kammala digirinsa da sakamako mai daraja ta farko a fannin tattalin arziki daga jami’ar Portsmouth.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwargidan Khalifan Tijjaniyan ce ta zuba kyawawan hotunansu yayin da suka dire garin Landan don taya kyakyawar budurwar murna a daren Laraba amma yanzu ta cire hotunan.

Sai dai shafin masoyan tsohon sarkin Kanon ya wallafa hotunan inda Legit.ng Hausa ta samo muku.

Ga wasu daga cikin hotunan:

Mustapha Sanusi ya gaji mahaifinsa yayin da ya kammala jami’a

A wani labari na daban, abun murna da farin ciki ya dira cikin iyalan Mai Martaba sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, a ranar Talata, 19 ga watan Yuli.

Lamarin mai dadi ya kasance ne bayan 1 cikin ‘ya’yansa maza mai suna Mustapha Lamido Sanusi, ya kammala karatunsa tare da samun digiri mafi daraja a bangaren tattalin arziki kamar mahaifinsa amma a jami’ar Birtaniya.

Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya tare da mata da ‘ya’yansa sun yi tattara har kasar Birtaniya domin halartar shagalin yaye daliban.

Ba a bar Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a baya ba, ya garzaya Birtaniya domin taya ‘dansu murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel