"Dole Ta Iya Larabci": Wani Dan Najeriya Ya Lissafo Sharrudan Da Matar Da Ke Son Auren Shi Za Ta Cika

"Dole Ta Iya Larabci": Wani Dan Najeriya Ya Lissafo Sharrudan Da Matar Da Ke Son Auren Shi Za Ta Cika

  • Wani mutum dan Najeriya wanda ke neman matan aure ya lissafa abubuwan da ke bukata a matar da ya ke so
  • Daya daga cikin abubuwa masu ban mamaki da ya lissafa a Twitter shine dole wacce zai aure ta iya magana da larabci
  • Wani sharadi da aka gani cikin jerin sharudan shine dole wacce ke sha'awar aurensa ta dole ta shirya tarewa a duk garin da mijin ke so

Mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da jerin sharruda na musamman da wani dan Najeriya wanda ke son aure ya lissafa.

A jerin sharrudan da ya wallafa a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, mai amfani da Twittan mai suna Banjo Hanjo ya ce dan uwansa na neman matan aure.

Matashi mai neman aure
"Dole Ta Iya Larabci": Wani Dan Najeriya Ya Lissafo Sharrudan. Hoto:Twitter/@banjohanjo4 da Junior Asiama / 500px/Getty Images. (An yi amfani da hoton namijin don misali ne kawai).
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma, akwai jerin sharudda da ya ke bukata matar da ke son aurensa ta cika.

Daya daga cikin sharudan shine duk matar da ke son aurensa ta kasance bata san wani namiji ba.

Ya kuma ce dole duk macen da ke son aurensa ta zama ta iya magana da harshen larabci sosai.

Ta kasance za ta iya kaura da shi zuwa duk garin da ya ke so

Wani abin ban sha'awa shine ya ce duk matar da ke son ta sace zuciyarsa ta kasance za ta iya canja gari kuma ya zama cewa bata yi soyayya da wasu maza a baya ba.

Ya bukaci duk wadanda ke sha'awar aurensa su yi magana, hakan ya janyo martani daga mutane da dama.

Ga rubutun da ya wallafa a Twitter:

Kara karanta wannan

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali

Martani daga masu amfani da Twitter

@gimbakakanda ya ce:

"Ka fada wa dan uwanka mai nuna wariyar launin fata da wariyar jinsi ya kai kansa asibiti."

@GirlLikeChoupi ya yi martani:

"Don Allah ta roki Ubangiji ya baka laka ta gina matar taka?"

@A_Kasrawi ya ce:

"Idan kun san wata mace da ta cika sharrudan nan ku sanar da ita kimarta saboda kada ta biye wa ja'irai irin wannan mutumin."

Bacin Rana: Matar Aure Ta Fallawa Mai Wasan Barkwanci Mari Bayan Ya Nemi Su Sha Soyayya A Bidiyo

Wata matar aure ta fusata bayan wani matashi ya isa gareta sannan ya nemi soyayyarta.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, mutumin mai suna Deehans ya tunkari matar sannan ya nemi ta bashi lambar wayarta.

Cikin mutunci ta ki amsa bukatar shi sannan ta sanar da shi cewa tana da aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel