Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Ɗakinsa Da Kaya a Hargitse

Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Ɗakinsa Da Kaya a Hargitse

  • Wani dan Najeriya ya koka a kafar sada zumunta inda ya ce yana bukatar matar aure yayin da ya wallafa hujjar da ta sa yake so ya yi auren
  • Matashin wanda nuna cewa shi malami ne ya wallafa bidiyon dakin sa kaca-kaca inda yace a duba a halin da yake ciki
  • Nan da nan mutane suka fara caccakar sa inda wasu ke ganin ba aure ya ke bukata ba, ya kamata ya fara kimtsa kan sa tukunna

Ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani sun dinga tsokaci a karkashin wata wallafar wani matashi ta bidiyon dakin sa wanda ya yi kaca-kaca.

Mutumin mai amfani da suna the_scholar1, ya garzaya shafinsa na Twitter inda ya ce yana matukar bukatar matar aure, hakan yasa ya wallafa bidiyon dakin na sa.

Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Cakuɗaɗen Ɗakinsa
Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Cakuɗadden Ɗakinsa. Hoto: @the_scholar1
Asali: Twitter

Dakin wanda babu haske a cikin sa ya yi kaca-kaca yayin da sutturun sa ke zube a kasa tare da sauran abubuwa.

Gadonsa kuwa ba a cewa komai, don takardu da sauran kayan datti ne a kan shi cunkus. Akwai bangaren da yake dauke da kura da sauran abubuwa.

Ga bidiyon da ya wallafa a kasa:

Wannan bukatar tashi ta dauki hankali kwarai inda mutane suka dinga sukarsa.

Tsokacin jama’a karkashin wallafar

Mutane da dama sun dinga tsokaci iri-iri karkashin wannan wallafar ta shi.

AbeniJade ya ce:

“Maimakon tona wa kan ka asiri, da ma ‘yar aiki ka samu. Da N3,000 ko N500 za ka samu mai gyara maka daki tare da yi maka wanki. Ina aiki don haka nake gaza yin ayyuka na saboda akwai wahala. Kudi kawai zaka biya a yi maka ayyuka. Ta yiwu matar ka ba ta da son yin aiki.”

maureen_dammy ta ce:

“Ya kamata ka gyara kan ka. Ka koyi halayyar mayar da kaya inda ka ajiye. Ka zabi rana daya cikin mako da zaka dinga kimtse-kimtse.
“Ya kake yi ka yi bacci a dakin nan? Ina mamakin yadda kicin ko ban dakin ka zai kasance.”

Ab_Ishaq ya ce:

“Ka gyara kan ka. Daki na yana cikin dakuna mafi kyau a cikin abokai na. Dayawan abokai na suna kawo baki idan sun kai mu su ziyara.”

masud_basheer ya ce:

“Ni ban ga laifin dakin nan ga namiji ba. Na fahimci ba ka kai mata dakin ka. Ni dai ban ga wani abu anan ba. Ka dinga gyara dakin ka ko da sau daya ne a wata.”

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel