Sheikh Zakzaky: Ina burin komawa Zariya na ci gaba da abin da nake yi a baya

Sheikh Zakzaky: Ina burin komawa Zariya na ci gaba da abin da nake yi a baya

  • Shugaban kungiyar yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya magantu a kan wasu lamura da suka shafi rayuwarsa
  • Zakzaky ya ce yana da burin komawa Zariya domin ya ci gaba da harkokinsa da yake yi a baya
  • Sai dai ya ce abun da ya sanya a gaba yanzu shine ganin ya samu lafiyar jikinsa domin ya ce a yanzu haka baya iya tafiya sai dai a kwashe shi

Babban malamin addini kuma shugaban kungiyar yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana cewa yana burin sake komawa garin Zariya domin ci gaba da harkokinsa na baya, musamman idan ya samu sauki daga rashin lafiyar da yake yi.

Sheikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da shashin Hausa na BBC.

Kara karanta wannan

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

Sheikh Zakzaky: Ina burin komawa Zariya na ci gaba da abin da nake yi a baya
Sheikh Zakzaky ya ce yana burin komawa Zariya ya ci gaba da abin da yake yi a baya Hoto: Premium Times

A cikin hirar tasu, Shehin malamin ya bayyana halin da yake ciki inda ya ce a yanzu daukarsa ake yi sakamakon dagargaza masa cinya da hannu da ya ce anyi.

Zakzaky ya ce:

“Daukata ake yi tun da an dagargaza min cinya ta dama, ba wai an karya ba an dagargaza min ita, haka hannuna ma na hagu an dagargaza shi."

Da aka tambaye shi kan adadin harsashin da yake tunanin an yi masa a hannu da kafar tasa, sai shehin Malamin ya ce, wuta wasu mutane hudu suka bude masu a cikin dan karamin dakin da suke, yana mai cewa:

“Ai harbe-harbe ne. Wato mutane ne suka tsuguna su huɗu suna ruwan harsasai a cikin ɗan ƙaramin ɗaki da muke.”

Da aka tambaye shi kan zargin da suke yi na cewa shugaban kasa ne ya yi umurnin far masu, Zakzaky ya ce:

Kara karanta wannan

Mu ne muka kashe kasar nan, ya kamata yanzu ina gidan kurkuku inji Tsohon Ambasada

“Ba zargi ba ne abin da ya faru kenan, kuma ai ya yi magana da aka tambaye shi ya ce Zakzaky ya yi gwamnati ne a cikin gwamnati.
“Me wannan kalma ke nufi? Ka ga ya nuna cewa laifin Zakzaky ne, a ganinsa shi ke da gwamnati ga kuma Zakzaky yana da gwamnati don haka zai rusa gwamnatin Zakzaky, ya wuce haka nan.”

Da aka tambaye shi game da abun da zai cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai idan ya hadu da, sai ya ce:

“ Zan ce musu su kammala ayyukan da suka fara, su ci gaba su cikata ladansu.”

Kan abun da kalamin nasa ke nufi, sai ya ce:

“Ba suna so su kashe ni ba ne, to ga fili ga mai doki.”

Game da ko ya nemi jin dalilin shugabannin na aikata abun da suka aikata masa, sai Zakzaky ya ce:

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

“Ai na sani. Mulki ne dai iyakarsa nan duniya ne, kwana nawa ne mulkin ai zai zo ya ƙare. Ita ma rayuwar za ta zo ta ƙare. ai lokacin da aka harbe ni wani minista cikin ministocin Buharin ya bugo min waya, na amsa an harbe ni ina kwance.
“Na ce masa ka ga abin da gwamnatinku ta yi min ko? Na ce masa ka ce ina gaida Janar Buhari, ku yi gwamnati lafiya, sai mun haɗu a lahira.
“Duk abin da za ku yi ku yi za mu tsaya a gaban Allah ranar gobe ƙiyama. Kuma ƙiyamar ba nisa gare ta ba.”

Kan ko yana da muradin komawa Zariya da sake gina muhalinsa, sai ya ce:

“In shaa Allahu ba abin da zai hana wannan. Amma da yake yanzu abin da yake gabanmu shi ne lafiyar jikinmu, amma in shaa Allah duk abin da muka rasa a Zariya za mu mayar da su kuma duk abin da ake yi za a ci gaba da yi.”

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

Zakzaky ya gurgunce, matarsa ta sukurkuce: Kungiya ta roki Buhari da ya basu damar fita kasar

A gefe guda, myun ji a baya cewa wata kungiya mai rajin kare hakkin bil'adama ta sanar da rashin lafiyar shugaban kungiyar shi'a ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenatuddin, inda suka ce a halin yanzu Zakzaky ya gurgunce, yayin da matarsa ke amfani da kujerar guragu.

A wata takarda da sakataren watsa labaran kungiyar, Mr Segun Fanimo ya sa hannu a ranar Alhamis a Kaduna, kungiyar ta shawarci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta jikan bil'adama, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel