Ku cire ni daga bakinku: Maishadda bai yaudare ni ba, babu komai tsakaninmu – Aisha Humaira

Ku cire ni daga bakinku: Maishadda bai yaudare ni ba, babu komai tsakaninmu – Aisha Humaira

  • Jarumar fim Aisha Humaira ta magantu a kan rade-radin da ake yi na cewa Maishadda ya yaudareta, ya ki aurenta
  • Humaira ta bayyana cewa hotunansu da aka gani tare wanda ya yi kama da na mata da miji ba na gaske bane, talla suka yiwa wani shago
  • Ta ce Maishadda abokinta ne kuma ba su taba furta kalmar soyayya a tsakaninsu ba balle har a kai ga yaudara

Shahararriyar jarumar Kannywood, Aisha Humaira ta yi karin haske kan alakarta da babban furodusar masana’antar wanda ya angwance a kwanan nan, Abubakar Bashir Maishadda.

Humaira ta bayyana cewa sabanin abun da mutane ke tunani, babu wani abu da ya danganci soyayya tsakaninta da Maishadda illa kawai abokin sana’arta ne da suka shaku.

Ku cire ni daga bakinku: Maishadda bai yaudare ni ba, babu komai tsakaninmu – Aisha Humaira
Aisha Humaira ta ce basu taba soyayya da Maishadda ba Hoto: realabmaishadda
Asali: Instagram

Mutane dai sun yi cece-kuce tun bayan bayyanar wasu hotunansu wanda ya yi kama da na aure, inda wasu da dama ke ganin cewa ya yaudari jarumar ne sannan ya je ya yi aurensa.

Kara karanta wannan

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

Jarumar a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta roki jama’a da su cire ta daga bakinsu a kan cewa furodusan ya ki aurenta ya je ya auri wata.

Ta ce:

“Barkarmu da war haka ina yi mana fatan alkhairi mai magana Aisha Humairah. Na fito ne zan yi magana a kan wasu kananan maganganu da suke ta kaiwa suke komawa. Da ban yi niyar yin magana ba amma wasu daga cikin yan uwana suka bani shawara ya kamata na fito na yi magana saboda maganganun da suke zuwa suke dawowa ya ishe su.
“Game da hotunan da muka yi kwanaki ni da Maishadda, mun yi hotunan wanda ake tunanin aure za mu yi shiyasa muka yi wannan hotuna. A’a ko daya ba haka bane, mun yi wadannan hotunan ne na tallar wani shago mai suna Shehu dan kwarai.

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

“A cikin bidiyon an bukci cewa za mu fito a kamar mata da miji, mun yi hotunan kafin aurenmu, sai kuma aka nuno mu kamar gamu nan ranar bikinmu. Wannan mun yi shi ne duk a cikin talla, wanda ranar da aka saki wannan hotunan an sake shi da safe sannan aka saki bidiyon da daddare saboda ya wankewa mutane tunanin da suke yi.
“Bidiyon na nan a kan page dina na Instagram duk wanda ya duba zai gani, hakazalika yana nan a kan page din Maishadda haka yan uwa da abokan arziki sun taya mu talla, yana nan a kan youtube din Maishadda wanda duk wani mai tunani mai hankali a matsayinsa na dan adam ya san cewa bidiyo ne aka yi san a talla.
“To ban san mai mutane suke so ba, kun zo kuna ta wasu kananan maganganu kuna cewa Maishadda ya yaudare ni da ni zai aura ya zo ya fasa, kwatakwata ni da Maishadda bamu taba soyayya ba wallahi, abokina ne shi tun kafin na fara fim, abokina ne bayan na fara fim da kuma zuwa yanzu. Da ni aka yi yawancin duk shirye-shiryen bikinsa sai kuma Allah ya ban samu damar zuwa ba, kowani dan adam yana da uzurinsa, wani abu ne ya taso mun sai ban samu zuwa bikin ba.

Kara karanta wannan

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

“To dan Allah dan Annabi ku cirewa kanku wannan kananan maganganun da kuka daura wa kanku, ni wallahi duk maganar da kuke yi bai dame ni ba saboda ni da shi da duk wanda ya sanmu ya cewa wannan maganar babu shi ba gaskiya bane.
“Hakazalika gabaki daya abokan sana’armu duk wanda ya sanmu ya san bamu tana soyayya da Maishadda ba ban taba son shi ba shima bai taba furta mun soyayya ba, iyakaci abokin sana’a ta ne wanda muke yawan tallace-tallace tare har zuwa yanzu aka nemi mu fito a matsayin mata da miji, don haka ku cire ni daga bakinku, don Allah dan Annabi ku daina yawo da ni kuna cewa Maishadda ya yaudare ni, ni wallahi bai yaudare ni ba iyakacina da shi abokin sana’ata ne, kuma abokin mu’amala ta ne, don haka ina fatan wannan bayani nawa zai kawo karshen cece-kucen.”

Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

A baya mun kawo cewa a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin babban furodusan masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jarumar fim, Hassana Mohammed.

Auren wanda aka daura a Masallacin Murtala da ke birnin Kano, ya samu halartan manyan jaruman masana’antar wadanda suka nuna kara sosai ga abokan sana’ar tasu.

Tun farko dai labarin auren ya ja hankalin jama'a duba ga yadda ba'a cika aure tsakanin yan fim ba, domin sun fi auren yan waje, illa yan tsiraru da suka kulla auratayya a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel