Na sha baƙar wahala: Jaruma mai maganin mata ta magantu kan kama ta da ƴan sanda su ka yi

Na sha baƙar wahala: Jaruma mai maganin mata ta magantu kan kama ta da ƴan sanda su ka yi

  • Jaruma, fitacciyar mai maganin mata ta yi bayani a wani bidiyo wanda ta wallafa a shafinta na Instagram akan rikicin ta da Ned Nwoko, dan kasuwa kuma dan siyasa da matarsa jarumar fina-finai, Regina Daniels
  • Tun a kwanakin baya wata tirka-tirkar sarkakiyar rigima ta rikice tsakanin Regina da Jaruma, inda Regina ta musanta amfani da magungunan matan da Jaruma ke sayarwa wurin mallake Nwoko da raba shi da matarsa
  • A lokacin Jaruma ta shaida cewa har kudi ta ba Regina don ta tallata mata kayan matan, sai dai bayan rigimar ta yi nisa Nwoko ya tura ‘yan sanda su kama Jaruma akan surutan da ta dinga yi akan shi

Fitacciyar mai sayar da magungunan mata, Jaruma ta saki wani bidiyo wanda ta yi bayani dangane da rikicin da ya shiga tsakanin ta da dan kasuwa kuma dan siyasa, Ned Nwoko da matarsa, Regina Daniels wacce fitacciyar jarumar fina-finan ce.

Kara karanta wannan

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

Dama Regina ta yi kira ga Jaruma tun a baya inda ta ce ba ta yi amfani da magungunan ta wurin mallake mijinta da kuma fitar da matarsa daga gidansa ba.

Na sha baƙar wahala: Jaruma mai maganin mata ta magantu kan kama ta da ƴan sanda su ka yi
Na sha wahala: Jaruma ta yi magana kan kama ta da 'yan sanda suka yi. Hoto: @Jaruma_empire
Asali: Instagram

Jaruma ta zargi Regina da damfararta ta hanyar amfani da magungunanta da kudin ta wanda ta ba ta don ta tallata mata kayan mata.

Ya yi bayani akan abin ya raba shi da tsohuwar matarsa

The Cable ta bayyana yadda a baya Nwoko ya musanta cewa matarsa tana amfani da kayan mata, ba kamar yadda Jarumar tace ba.

Sannan ya yi karin bayani akan yadda auren sa ya rabu da tsohuwar matarsa, Laila Charani, ‘yar kasar Morocco. Ya ce sun rabu ne saboda halayen ta ba kayan matan Jaruma ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa wata budurwa hukuncin kisa kan tura sakon batanci ga Annabi a Whatsapp

A bidiyon da Jaruma ta yi, ta ce Nwoko ya yi amfani da ‘yan sanda wurin cutar da ita, kama ta da kuma tsare ta.

Ta ce an cuce ta ana neman hana ta kuka

Kamar yadda ta ce:

“Na wahala. Na kasa gane yadda mutum zai cutar da kai idan kuma ka rama sai ya nemi dawowa kan ka. Sai su yi amfani da ‘yan sandan Najeriya don su cuce ka kuma su rufe maka bakin ka.
“Ka kwace filin wani ko gonar sa. Idan ya yi korafi sai ka tura ‘yan sanda su kama shi ka kuma kulle shi. Na biya kudi Naira miliyan 10 don a yi min aiki amma an ki yi. Na yi korafi kuma an kama ni.
“Matasan Najeriya nawa ku ke so ku sa a gidan yari? Idan aka nemo sunan ka a yanar gizo, yawan mutanen da ka kulle kadai za a gani. Wa kake so ya zabe ka?”

Kara karanta wannan

'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Online view pixel