'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki

'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki

  • Wata mata ta kai karar yar aikinta da ta arce mata da makudan kudi da sarka bayan mako guda da fara aiki
  • Matar ta ce mai aikin yar jihar Cross Rivers ce kuma an nemeta sama da kasa yanzu an rasa
  • Wanda ya hada ta da yarinyar kuma yace babu ruwansa saboda irin haka ya taba faruwa a baya kuma ya ji jiki hannun jami'an tsaro

V.I - Wata mai aiki mai suna Blessing, ta arce da kudi da sarkokin kimanin miliyan goma sha hudu (N14m) daga gidan maigidarta dake unguwar Victoria Island, jihar Legas.

Maigidar, Pearl Ogbule, a ranar Talata ta bayyana cewa Blessing ta kwashe mata dukiya ne kimanin mako guda bayan fara aiki da ita, rahoton Punch ta ruwaito.

Ta ce tun lokacin suka bazama nemanta amma har yanzu babu labarinta.

Kara karanta wannan

Mijina yana cizo na, ya lakaɗa mun duka idan ban yi abinci ba, Mata ta nemi kotu ta raba auren

'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m
'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki Hoto: Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Pearl Ogbule tace bayan karbanta aiki, sun yanke shawaran kaita ofishin yan sanda don yi mata rijista.

Amma yayinda take shirin zuwa, Blessinga ta gudu da kudinta.

Tace:

"Ta fara aiki da ni misalin karfe 8:30 na daren Lahadin da ta gabata. Da na dawo daga wajen wani taro, na shiga cikin gida kuma na kira mahaifina ya bude kofa. Amma lokacin da ya sauko bude min, yace ai kofar bude take.
"Sai mahaifina ya shiga dakin Blessing kuma ya ga ta kwashe kayanta ta gudu."
"Na kira wanda ya hada ni da ita amma yace ba zai so ya taya ni nemanta ba saboda irin haka ya taba faruwa da shi kuma aka daureshi kurkukun yan sanda. Na kai kara ofishin IRT da DSS.'

Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi

Kara karanta wannan

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

A wani labarin kuwa, wani mutum dan Najeriya ya nuna karamci ga wata budurwa wacce ta damfare shi N500,000 tun shekaru 5 da su ka shude.

Ikechukwu Diamond, a cikin wata wallafa mai tsawo da ya yi a LinkedIn, ya bayyana matar ta zo neman aiki a wani kamfani da ya ke cikin masu daukar aikin.

Tana shigowa harabar wurin ya gane ta daga nan ya umarci jami’an tsaron kamfanin da kada su bar kowa ya fita daga wurin.

Ta yi matukar mamakin yadda ya yi bayan lokacin da za su tattauna ya bata dama duk da ta tabbatar ya gane ita ce ta damfare shi a baya.

Ta na ganin haka ta durkusa gwiwoyi bibbiyu tana hawaye. Ba tare da ta yi zato ba, mutumin ya rungume ta ya kwantar ma ta da hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel