Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

  • Wata ‘yar Najeriya da ke kasar waje ta samu masoyin hakika kuma ta yi auren ta duk da ta kai shekaru 61 da haihuwa
  • Matar mai suna Lizzy Taiwo ba ta taba aure ba a rayuwar ta balle har ta kai ga haihuwa, ta samu miji na gani da fadi
  • Lizzy ta auri babban abokin ta da ke kasar Jamus inda aka yi shagali na gani da fadi wanda abokai da ‘yan uwa su ka taya su murna

Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 61, mai suna Lizzy Taiwo, ta fita daga kasuwar ‘yan mata inda ta zama matar aure cikin kwanakin nan ga babban abokinta Colins.

Instablog9ja ta wallafa hotuna da bidiyoyin bikin wadanda aka ga amaryar da bata taba haihuwa ko kuma aure ba a rayuwarta.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Buhari ta taimakawa mutane sama da 500, 000 inji Dr. Isa Pantami

An yi auren tsakanin Lizzy da Collins ranar Asabar, 15 ga watan Janairu a can cikin kasar Jamus.

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus
Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus. Hot daga @Instablog
Asali: Instagram

‘Yan uwa da abokan arzikin ma’auratan sun je don taya su murna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga yadda Lizzy ta sanya wata farar riga irin ta amare ta na kwasar rawa tare da angon ta a gefen ta.

Tsokacin jama'a

Nan da nan mutane suka fara tsokaci karkashin bidiyon.

@thriftinnaija ya ce:

“61 a ina? Ina fatan ba za ta fara tsofewa yanzu da ta yi aure ba. Ina mata barka.”

@ut_mimigal ta ce:

“Wadannan ya kamata su dawo gida su samar wa masu kananun shekaru wuri. Ni ban gane batun aure ba a nan.”

@denzuluche ya ce:

“Amma iyaye na suke matsa min a kan in yi aure. Wanda yanzu zan iya dirka wa diyar wani ciki in ya so daga bisani na aure ta.”

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa wata budurwa hukuncin kisa kan tura sakon batanci ga Annabi a Whatsapp

@dr_samsurge ya ce:

“Toh ba laifi, amma shekaru 61, hmmm... ko shekaru 70 mutum ya kai zai iya yin auren sa.”

Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata

A wani labari na daban, wasu maza biyu sun zama ababen kwatance bayan irin yadda su ka nuna kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu wacce ba a samu a wurin maza sai dai dai.

Daya yana auren wata mata ne wacce tsohuwar matar dayan ce, amma kyakkyawar alakar ta su sai da ta ba mutane da dama mamaki. Cikin jin dadi ya siya wa mijin tsohuwar matarsa wani takalmi mai kyau da kuma kayatarwa.

Har zubar da hawaye mutumin ya yi a wani bidiyo wanda tsohuwar matarsa ta wallafa a Instagram, inda aka ga yadda mutumin ya ke godiya ga mijin tsohuwar matarsa tare da wasu yara da ake zargin yaransa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel