Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
An yi sulhu tsakanin Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo). An yi hakan bayan Oshiomhole ya zargi Akpabio da karya yarjejeniya.
An zargi jami'an NDLEA da kashe Faisal Yakubu Hussaini a Dangi, jihar Filato, yayin da suka kai samame a gidan saukar baki. Hukumar ta yi martani kan wannan zargi.
Matasa masu zanga-zanga sun durfafi Majalisar Tarayya domin bukatar a kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari saboda wasu matakai da ke jefa al'umma cikin kunci.
Saboda matsalar lantarki a Najeriya akwai, gwamnonin jihohin Gombe da Osun sun fara ƙoƙarin samar da lantarki domin rage dogaro da gwamnatin tarayya.
Stephen Abuwatseya, wani direban Bolt a Abuja, ya ba da haƙuri ga ɗan majalisar Abia, Alex Ikwechegh, bayan wata rigima ta ɓarke tsakaninsu kan kai masa sakon kaya.
Gwamnatin Katsina karkashin gwamna Dikko Radda ta yaye askarawan yaƙi 500 karo na biyu. Hakan na zuwa ne bayan Lakurawa sun ɓulla a yankin Arewa ta Yamma
Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya ce babu inda dokar Najeriya ta haramta gurfanar da yara idan har suka saba ka'ida a kasar inda ya ce komai a cikin doka yake.
Gwamnatin tarayya ta ƙaryata labarin cewa babbar tashar wutar lantarki a kasar nan ta sake lalacewa a karo na 11 a 2024 duk da har yanzu ana fama da rashin wuta.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya sake ba da umarnin gyara ƙarin asibitoci bayan guda 102 da da ke aikin inganta su a faɗin kananan hukumomi.
Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin N549bn na shekarar 2025. Bangaren ilimi da kiwon lafiya sun fi samun kaso mai tsoka a kasafin kudin Kano.
Labarai
Samu kari