Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
An yi sulhu tsakanin Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo). An yi hakan bayan Oshiomhole ya zargi Akpabio da karya yarjejeniya.
Hukumar Inshorar Bankuna ta Najeriya (NDIC) ta sanya 4 ga watan Disamba, 2024 matsayin ranar da za ta sayar da kadarorin bankin Heritage. Ana neman masu saye.
Sanatan Neja ta Gabas, Mohammed Sani Musa ya ce ba a fahimci abin da yake nufi ba kan cire tallafin mai, ya ce wasu mutane kalilan ke cinye kudin da ake warewa.
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya, (IPMAN), ta cimma matsaya da matatar man Dangote domin fara jigilar man fetur kai tsaye.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya raba ababen hawa ga shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano. Sanata Barau ya ba da motoci da babura.
Kungiyar kwadago ta ce yunwa ta fara haifar da cututtuka kama su kwashoko a Najeriya. NLC ya ce akwai bukatar fitar da tare tsaren kawo saukin rayuwa.
Rahotannin sun nuna cewa da tsakar dare wayewar garin yau Litinin, wasu miyagun ƴan bindiga suka kashe mutum biyu a Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shiga tsakani domin kawo karshen dambarwar da ke tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin wutar lantarki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Riyadh da ke Saudiyya domin halartar taron Larabawa da kasashen Musulunci inda za a tattauna muhimman batutuwa.
An fara shirye-shiryen gudanar da jana'izar tsohon shugaban hafsan sojojin kasan Najeriya (COAS), Taoreed Abiodun Lagbaja. Za a binne marigayin a Abuja.
Labarai
Samu kari