Majalisar dattawa ta kasa ta amince a hana mutane talla da yin wa'azi a cikin motocin haya a Najeriya. Za a rika cin tarar duk wanda ya yi haka N50,000.
Majalisar dattawa ta kasa ta amince a hana mutane talla da yin wa'azi a cikin motocin haya a Najeriya. Za a rika cin tarar duk wanda ya yi haka N50,000.
Abokiyar aikin Mary Habila budurwar da ta mutu a gidan Ministan ayyuka, ta bayyana abubuwan da suka faru. Ta ce ta yi bayani ne ba tare da an matsa mata lamba ba.
Gwamnatin Katsina ta yabawa sojoji kan farmaki da suka kai kan gagga gaggan 'yan bindiga Manore da Lalbi a Bichi. Sojoji sun musu ruwan wuta ta sama da kasa.
Bako Wurgi, hatsabibin shugaban 'yan bindiga kuma na hannun daman Bello Turji, ya mutu sakamakon raunukan harbi, bayan ya ba sojoji bayanan sirri.
Gwamnatin tarayya ta waiwayi mutanen jihar Jigawa. An kaddamar da karasa aikin tsohon gwamna, Saminu Turaki. Mutane sama da akalla kusan miliyan 1.5 za su amfana.
Bullar ƙungiyar Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma na zama babban barazana ga shugabannin yan bindiga wanda ka iya zama tashin hankali tsakaninsu.
NSCDC ta tura jami’ai 1,850 zuwa Kogi don ba da tsaro a lokacin bukukuwan karshen shekara. An bukaci jama’a su ba jami'an hadin kai domin wanzar da zaman lafiya.
Gwamnatin tarayya ta dakatar da nada Akanta Janar da Bola Tinubu ya nada. Hajiya Naja'atu Muhammad ta ce an ware wasu 'yan Arewa biyu wajen nada shi.
Dan majalisar Kaduna ya ce kudin jama'a na zurarewa ta ko'ina, ta hanyar kasadin kudin shekara-shekara. Ya ce bai dace a rika barnar kudin 'yan Najeriya ba.
Yan kasuwa sun bayyana cewa daga nan zuwa makon gobe ƴan Najeriya su fara shan mao da arha fiye da farashin yanzu sakamakon ragin matatar Ɗangote.
Farashin shinkafar gida ya ragu da kashi 10 a Enugu; wanda ya sanya mutane farin ciki gabanin Kirsimeti, yayin da dillalai ke ba da shawarar saye kafin ta kara kudi.
Labarai
Samu kari