Babbar Kotun Tarayya ta ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami, bayan ta amince da buƙatar hukumar EFCC.
Babbar Kotun Tarayya ta ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami, bayan ta amince da buƙatar hukumar EFCC.
Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da cewa mutanen karamar hukumar Bichi sun kama dan bindiga bayan an yi kukan kura an kama shi da kayan sojoji.
Shugaba Tinubu da gwamnoni sun bukaci 'yan Najeriya da su rundumi soyayya, zaman lafiya, da hadin kai yayin bikin Kirsimeti. Diri ya nemi a taimaki marasa galihu.
Barayi sun haura katanga, sun sace akuyar Kirsimet a Gwagwalada da ke Abuja. Mai akuyar ya kai rahoto yayin da ‘yan sanda suka soma bincike don gano barayin akuyar.
Gwamnan jihar Ribas ya rattaba hannu tare da umartar a bai wa ma'aiksta da ƴan fansho alawus na N100,000 domin su yi shagalin bikin kirsimeti cikin walwala.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ya koka kan yawaitar hadurran motan da ake samu. Ya ce suna jawo asarar rayuka masu yawa.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Imo, sun fafata da wasu 'yan bindiga da ake zargin na kungiyar IPOB ne. Jami'an tsaron sun hallaka mutum uku daga cikinsu.
Sanata Oluremi Tinubu, uwar gidar shugaban Najeriya ta bukaci ƴan Najeriya su nunawa juna kauna, tausayi, ta ce ranakun farik ciki da jim daɗi na nan tafe.
Kusa a jam'iyyar PDP, Bode George, ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wankin babban bargo. Jigon na PDP ya zargi Tinubu da rashin nuna tausayi ga yan Najeriya.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi martani kan rikita-rikitar da ake yi kan shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci inda ya ce zai tabbatar da bin tsarin doka.
Gwamna Mai Mala Buni ya dauki ma'aikatan lafiya kimanin 424 a jihar Yobe domin inganta rayuwar al'ummar jihar. Ya ce zai cigaba da kula da harkar lafiyar al'umma.
Labarai
Samu kari