Mawakin Siyasa Ya Watsa wa Abba Kabir Kasa a Ido kan Saka Shi a Kwamitin Kamfe
- Mawaƙi kuma ɗan siyasa a Kano, ya ƙi amincewa da shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Abba Yusuf.
- Matashin ya ce ba a tuntube shi ba kafin saka sunansa cikin jerin waɗanda aka naɗa, saboda haka ba zai shiga ayyukan kwamitin ba
- Duk da haka, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da goyon bayan APC da ƙungiyar Arewa for Asiwaju wajen zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani mawakin siyasa, Jamilu Garko ya ƙi amincewa da naɗinsa a kwamitin kamfen Abba Kabir Yusuf.
An nada Jadda ne a matsayin mataimakin darakta a ɓangaren nishaɗi na kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Shugaban tawagar yaƙin neman zaɓen Da Hannuna a ƙarƙashin ƙungiyar Arewa for Asiwaju ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar da Punch ta samu.

Kara karanta wannan
Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?
Dalilin Garko na kin shiga kwamitin
Garko ya bayyana cewa ba a tuntube shi ba kafin saka sunansa cikin jerin waɗanda aka naɗa.
Ya ce ba zai shiga ayyukan kwamitin ba har sai an tuntube shi yadda ya kamata game da naɗin.
A cewarsa, da tawagar gwamnan ta tuntube shi kafin sanar da naɗin, da ya ba da shawarar wani mutum da zai riƙe matsayin maimakon shi.
An saka sunan Garko a matsayi na 169 cikin jerin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan, ƙarƙashin ɓangaren nishaɗi.
Duk da ƙin amincewa da naɗin, Garko ya gode wa Yusuf bisa ganin ya cancanci wannan matsayi. Ya ce zai ci gaba da goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ƙoƙarin ganin ta yi nasara a babban zaɓen 2027.
Ya ce:
“Ina godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ganin na cancanci wannan naɗi. Sai dai, ba a tuntube ni ba kafin saka sunana cikin jerin, kuma ba zan amince da naɗin ba har sai an tuntube ni.

Kara karanta wannan
Shin Tinubu ya karya doka da ya ce ba zai je kamfe wasu jihohin Najeriya ba? An samu bayani
“Zan ci gaba da ƙoƙari tuƙuru domin nasarar APC, amma ba zan shiga ayyukan kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Yusuf ba.”

Source: Facebook
Rawar da Jadda ke takawa a siyasa
Garko, wanda ya shahara a fannin nishaɗi a Arewacin Najeriya, ya yi suna wajen amfani da waƙoƙi domin haɗa kan ’yan siyasa da yaƙin neman zaɓe.
A matsayinsa na shugaban tawagar Da Hannuna a ƙarƙashin ƙungiyar Arewa for Asiwaju, ya taka rawa wajen ƙoƙarin tattara goyon baya ga takarar Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu.
Ya sake jaddada cewa yana nan daram wajen goyon bayan APC da ƙungiyar Arewa for Asiwaju gabanin babban zaɓen 2027.
Daurawa da malaman da suke kwamtin kamfen Abba
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Kano ta fitar da sunayen mambobin kwamitin ba da shawarwari kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna gabanin zaɓen 2027.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci kwamitin, yayin da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, zai zama mataimakin shugaban kwamitin.
Daga cikin waɗanda aka sanya akwai fitattun malaman addinin Musulunci, ciki har da Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Legit.ng