Akwai Kura: Bayan Shekara 12, Kamfanin Uber Ya Dakatar da Ayyukansa a Najeriya

Akwai Kura: Bayan Shekara 12, Kamfanin Uber Ya Dakatar da Ayyukansa a Najeriya

  • Uber ya sanar da cewa zai kawo ƙarshen ayyukansa a Najeriya daga 2 Metaga Satumba 2026, bayan ya shafe sama da shekaru 12 yana aiki a ƙasar.
  • Kamfanin ya fara aiki a Legas a shekarar 2014, inda ya ce ya ji daɗin kasancewa cikin rayuwar yau da kullum ta masu amfani da manhajarsa
  • Shugaban Uber, Dara Khosrowshahi, ya kuma sanar da rage ma’aikata kusan kashi 10 cikin 100, kwatankwacin mukamai 3,300

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Legas, Najeriya - Shahararren kamfanin jigilar fasinjoji, Uber, ya sanar da dakatar da ayyukansa a Najeriya.

Kamfanin na Uber ya sanar da cewa zai dakatar da ayyukansa ne daga ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2026.

Kamfanin Uber ya bar Najeriya
Wata mota mai dauke da tambarin Uber Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamfanin Uber ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan gudanar da cikakken nazari kan ayyukansa a ƙasar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu ya barke da murna bayan Najeriya ta samu wani cigaba

Uber ya fara gudanar da ayyukansa a Najeriya ne a shekarar 2014, lokacin da ya fara aiki a birnin Legas.

Uber ya yi bankwana da masu amfani da shi

Kamfanin Uber ya bayyana cewa dakatar da ayyukansa zai fara aiki daga ranar 2 ga Satumba 2026.

Uber ya ce:

“Muna rubuto wannan saƙo ne domin sanar da ku wani labari mai wahala. Bayan cikakken nazari kan harkokin kasuwancinmu, mun yanke shawarar kawo ƙarshen ayyukanmu a Najeriya daga 2 ga Satumba 2026.”

Kamfanin ya ce tun lokacin da ya fara aiki a Legas a shekarar 2014, ya ɗauki kasancewarsa wani ɓangare na rayuwar yau da kullum ta ’yan Najeriya a matsayin babban abu.

Ya ce manhajar ta taimaka wajen haɗa mutane da direbobin da ke ba da hidimar sufuri mai zaman kanta, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Kamfanin Uber ya yi godiya

Uber ya kuma gode wa masu amfani da manhajar bisa amincewarsu da kamfanin wajen haɗa su da direbobi domin isa wuraren da suke son zuwa cikin aminci, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Kamfanin ya amince cewa matakin na iya kawo cikas ga tsarin zirga-zirgar masu amfani da shi, sannan ya nemi afuwar waɗanda za su fuskanci matsala sakamakon ficewarsa daga Najeriya.

Kamfanin Uber ya dakatar da ayyukansa a Najeriya
Wata matashiya na kokarin shiga mota Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Uber ya sanar da sallamar ma’aikata 3,300

A wani lamarin kuma, kamfanin Uber ya sanar da cewa zai rage yawan ma’aikatansa da kusan kashi 10 cikin 100, wanda ya yi daidai da kusan mukamai 3,300.

Shugaban kamfanin na Uber, Dara Khosrowshahi, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya aikewa ma’aikatan Uber ranar Laraba.

Direban Uber ya cinye abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata matashiyar 'yar Najeriya ta bayar da bayani kan yadda ta kaya tsakanin kawarta da wani direban Uber.

Dirama ya barke bayan kawarta ta tura direban Uber ya karbo mata abincin Sallah daga wajen wata kawarta.

Direban Uber din ya gaggauta kawo karshen tafiyar tasa, sannan ya sace abincikin tare da tura sakon ban hakuri bayan ya cinye abincin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng