Rayuwar direbobin Uber a Najeriya

Rayuwar direbobin Uber a Najeriya

Uber wani kamfani ne wanda aka kafa a kasar Amurka a shekarar 2009. Kamfanin yana da wani application na waya wanda ke hada direba da kuma motar Taxi din da yake son ya fita da ita. Kamfanin yana aiki a kasashe 66, harda Najeriya, da kuma garuruwa 449 harda Abuja a ciki.

Rayuwar direbobin Uber a Najeriya
Direban Uber

Legit.ng ta samu wani rahoto na musamman akan direbobin Uber uga 3; Samuel, Adeleke da kuma Simon, wanda suka bayyana yadda kasuwancin ke tafiya da yadda Uber ke shigo da sabbin hanyoyin kasuwanci a Najeriya.

 

Masaniyar su tare da Uber

Samuel ya bayyana yadda ya hadu da Uber inda ya bayyana cewa ada yana aiki ne da wani Kamfani inda sai ga Uber ta shigo garin Abuja. Ya bayyana cewa a yanzu yana amsar kimanin Naira 100,000 a wata. Ya bayyana cewa aikin yana da kyau kuma yana duba izuwa gaba domin shima ya sayi motar shi kuma ya zama direban ta.

Ya bayyana cewa sauran motocin Taxi suna cargin mutum Naira 5,000 daga garin Abuja zuwa filin jirgin sama. Amma uber tana cargin mutum Naira 3000 ne kacal daga filin jirgin zuwa cikin birnin tarayyar.

Simon ya bayyana cewa ada yana aiki ne da wani kamfani a cikin Abuja. Yace "Yanzu yara na suna zuwa makaranta mai kyau kuma ina fatan in zama uba na gari". Ya bayyana cewa yana samun tsakanin Naira 90,000 zuwa 110,000 a wata.

 

Daga jakadan Uber

Abdulbaqi Jari yana daya daga cikin jakadojin Uber a Najeriya. Ya bayyana cewa Uber ba kamar kowanne taxi bane, domin kuwa suna da direbobi masu ili, da kuma sanin kanaiki. Ya bayyana cewa kuma Uber nada motoci masu kyau kuma masu lafiya.

Rayuwar direbobin Uber a Najeriya
Jakadan Uber

 

Kudaden shiga daga waje

Kamfanoni na duniya da yawa a yanzu suna shirin su shigo najeriya domin suyi kasuwanci a nan. Suna shigo garuruwa irin su Abuja da Lagos wadanda suna cikinmafi habbaka yanzu a duniya ma baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel