Peter Obi Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Abin da Ya Assasa Talauci a Najeriya

Peter Obi Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Abin da Ya Assasa Talauci a Najeriya

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi tsokaci kan matsalar talauci da ake fama da ita a Najeriya
  • Peter Obi ya bayyana cewa 'yan Najeriya ne da kansu suka zabi jefa kasar cikin talauci saboda irin abubuwan da suke aikatawa
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana shawarar da aka ba shi domin ganin an gyara Najeriya yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya yi magana kan matsalar talauci a Najeriya.

Peter Obi ya bayyana cewa matsalar talauci a Najeriya ba rashin albarkatun kasa ba ne, face sakamakon irin zaɓin da ƙasar ta yi ne.

Peter Obi ya koka kan matsalar talauci a Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Peter Obi ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026, yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ƙwararrun ma'aikata da masu sana'o'in hannu na Najeriya (ASVAN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Obijuru Everest.

Kara karanta wannan

Ana azumi Sanata ya gano laifuffukan da ba za su kai 'yan siyasa shiga wutar jahannama ba

Me Peter Obi ya ce kan talauci a Najeriya?

Ya bayyana cewa ƙasar da Allah ya ba man fetur, iskar gas, da kuma dimbin jama'a masu kuzari bai kamata ta kasance cikin wahala irin wadda Najeriya ke ciki ba.

A cewarsa, ainihin matsalar ita ce shugabanci da kuma al'adar da ke girmama cin hanci da rashawa maimakon yaƙarsa, jaridar Leadership ta kawo labarin.

"Muna cikin talauci ne saboda mun zaɓi mu kasance matalauta. Muna ba wa waɗanda suke sace kuɗin jama'a lakabin girmamawa da kujerun gaba a taro, sannan kuma muna tsammanin za mu bunƙasa."

- Peter Obi

Peter Obi ya kwatanta Najeriya da Indonesia

Ya kwatanta Najeriya da kasar Indonesia, wadda ya bayyana a matsayin ƙasa mai girma da yawan jama'a kusan ɗaya da Najeriya, amma tana samun nasarar tattalin arziƙi fiye da Najeriya saboda ƙwaƙƙwaran shugabanci da kuma sanya muhimman abubuwa a gaba.

Domin gyara Najeriya, Peter Obi ya ba da labarin yadda shugaban ƙasar Indonesia ya ba shi shawarar yaƙar satar kuɗin jama'a, zuba hannun jari a fannin ilimi da kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba da ya yi murabus ya zama Shugaban APC bayan awanni a Kano

Ya ce ƙasashen da ke bunƙasa ta hanyar da za ta dore suna mayar da hankali ne ga mutane da ƙananan masana'antu, inda ya jaddada cewa ƙananan masana'antu suna bunƙasa ne kawai a inda gwamnati ta samar da tsarin da ke da tabbas kuma babu yaudara.

Peter Obi ya ba 'yan Najeriya shawara
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Wadanne shawarwari ya ba da?

“Ku haɗa hannu a yaƙin neman samar da babbar Najeriya. Ku daina bauta wa waɗanda suke sace muku kuɗi, ku daina ba su lakabin girmamawa, kuma ku tsaya tsayin daka kan abin da yake daidai."
"Ku yi zaɓe, ku kare ƙuri’un ku, kuma ku taimaka wajen samar da shugabanni nagari a kowane mataki, tun daga kansila har zuwa shugaban ƙasa, idan kuka yi haka za ku ga ƙasar ta canza."

- Peter Obi

'Yan bindiga sun farmaki Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun farmaki tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, a jihar Edo.

Shugaban kungiyar Obedient Movement, Yunusa Tanko ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin an dauko hayarsu don kisan kai ne suka farmaki Peter Obi tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar ADC.

Lamarin ya faru ne lokacin da Peter Obi da sauran shugabannin ADC suka halarci taron shelar komawar Barrister Olumide Akpata zuwa jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng