Gwamnatin Trump Ta Yabawa Tinubu kan Daure 'Yan Ta'adda 386

Gwamnatin Trump Ta Yabawa Tinubu kan Daure 'Yan Ta'adda 386

  • Gwamnatin Amurka ta yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gurfanar da wasu da aka zarga da aikata ta'addanci a Najeriya tsawon shekaru
  • Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sunday Dare ya yi magana kan yabon da Amurka ta yi wa gwamnatin Najeriya kan masalar tsaro
  • Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a na kasa, Lateef Fagbemi ya sanar da cewa an gurfanar da sama da mutum 500

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Babban mai ba shugaba Donald Trump shawara kan harkokin kasashen Larabawa da Afirka, Massad Boulos ya yabawa gwamnatin Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta yi madalla da bayanin da gwamnatin Amurka ta yi kan kokarin da Najeriya ke yi wajen hukunta 'yan ta'adda.

Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu
Shugaba Donald Trump a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanan da hadimin Trump ya yi game da gwamnatin Najeriya ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi dalili 1 da ya jawo aka tashi baram baram a zaman sulhu da Amurka

Yabon da Amurka ta yi wa Najeriya

Amurka ta yaba wa gwamnatin Najeriya bisa jajircewarta wajen gaggauta shari’o’in da suka shafi ta’addanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da shi.

Sanarwar Amurka ta ce:

"Muna maraba da hukuncin da aka yanke wa ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin addini 386 a wasu shari’o’i da suka dade suna fuskantar jinkiri a kotuna.
"Muna ganin cewa gudanar da shari’o’i cikin lokaci kuma a bayyane yana da matuƙar muhimmanci wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da cibiyoyin shari’a."

Ta kara da cewa:

"Kiyaye dokar ƙasa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kuma tsaron dukkan ‘yan Najeriya."

Martanin Najeriya ga Amurka

Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Sunday Dare ya wallafa wani sako a X yana maraba da yabon da Amurka ta yi, inda ya ce:

"Wannan na nuna sabon ƙudurin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka wajen magance ta’addanci.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An nemi a yi wa Trump gwajin kwakwalwa kan yakin Iran

"A kowane ɓangare, shugaban ƙasa na yin duk mai yiwuwa domin kawar da ‘yan ta’adda a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyi."
Massad Boulos tare da Bola Tinubu
Massad Boulos na gaisawa da Bola Tinubu a Paris a 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

‘Yan ta’adda da aka yi wa hukunci

Gwamnatin Najeriya ta samu nasarar yanke hukunci ga mutane 386 da ake zargi da ta’addanci bayan gudanar shari’a a Kotun Tarayya da ke Abuja.

Ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya ce an gurfanar da mutane 508 a gaban kotuna 10 cikin kwanaki huɗu, inda aka yanke wa waɗanda aka samu da laifi hukuncin ɗaurin shekaru daga biyar zuwa rai da rai, gwargwadon girman laifinsu.

Ya ce an sallami mutane takwas, yayin da aka wanke biyu daga zargi, yana mai bayyana hakan a matsayin hujja ta bin ƙa’ida da adalci a shari’ar.

VON ta wallafa cewa Fagbemi ya ƙara da cewa an dage shari’o’i 112, kuma za a ci gaba da sauraron su a zagaye na gaba daga ranar 15 zuwa 18 ga Yuni, 2026.

Shugaban Amurka ya caccaki Fafaroma

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump na cigaba da caccakan mutanen da suke adawa da yake-yaken da ya ke yi.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

A wannan karon, Donald Trump ya dura kan Fafaroma Leo, inda ya bukaci shugaban addinin ya mayar da hankali kan aikin da aka nada shi ya yi.

A sakon da ya fitar, Trump ya nuna cewa ya yi wa Fafaroma Leo gata wajen nada shi da aka yi a 2025 bayan mutuwar Fafaroma Francis a Vatican.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng