Yakin Iran da Abubuwan da Suka Jawo Karancin Lantarki a Najeriya

Yakin Iran da Abubuwan da Suka Jawo Karancin Lantarki a Najeriya

  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan katsewar wutar lantarki, ya kuma yi alkawarin samun sauƙi
  • Ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya bayyana matakan da za su rage matsalar wuta a Najeriya
  • Adelabu ya sanar da cewa rashin wutar lantarki na shafar harkokin yau da kullum a kasar nan, lamarin da zai saka a dauki matakin gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan yawan katsewar wutar lantarki, tare da yin alkawarin cewa za a samu gyara a fadin ƙasar nan cikin kwanaki masu zuwa.

Ministan makamashi na kasa, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai inda ya yi bayani kan nasarorin da ya samu cikin shekaru uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Sheikh Khalifa Zariya ya rasu, Atiku ya yi magana

Ministan makamashin Najeriya
Ministan makamashi tare da ma'aikatar lantarki. Hoto: @IkejaElectric|@BayoAdelabu
Source: Twitter

Wutar lantarki ta yi karanci a Najeriya

A wani rahoto da tashar Channels Television ta wallafa, Ministan makamashin Najeriya ya ce matsalar da ake samu a kan lantarki ta wucin gadi ce.

Ya ce:

“Ina neman afuwar ‘yan Najeriya a hukumance, ni a matsayina na ministan wutar lantarki, kan wannan matsala ta wucin gadi da ke jawo wahalhalu, musamman a wannan lokacin na tsananin zafi,”

Ya ƙara da cewa kasuwanci, makarantu da masana’antu duk sun fuskanci matsala sakamakon katsewar wutar, yana mai cewa ba burinsu ba ne su tsinci kansu a irin wannan hali, amma akwai wasu dalilai da suka fi ƙarfinsu.

Mene ne dalilin rashin wuta a Najeriya?

Ministan ya danganta matsalolin da ake fuskanta yanzu da ƙarancin iskar gas da ake bai wa kamfanonin samar da wutar lantarki, sakamakon dimbin bashin da masu samar da gas ke bi.

Vanguard ta rahoto cewa ya yi ishara da cewa rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya na iya ƙara tsananta matsalar wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya janye kai mummunan hari Iran, ya fadi dalilan daukar matakin

A ‘yan makonnin nan, ‘yan Najeriya sun ci gaba da fuskantar katsewar wutar lantarki, lamarin da ya sa ake kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.

Wani rumbun wutar lantarki a Najeriya
Wata tashar wutar lantarki a Najeriya. Hoto: @TCN_NIGERIA
Source: Twitter

Bangaren wutar lantarki a Najeriya ya fi dogaro ne da tashoshin da ke amfani da iskar gas, amma suna yawan fuskantar tangarda sakamakon ƙarancin gas, gyaran bututun mai, tsofaffin kayan aiki da kuma matsalar kuɗi.

“Wadannan matsaloli na rage yawan gas da ingancinsa da ake kaiwa tashoshin wuta, wanda ke janyo ƙarancin samar da wuta da kuma yawaitar katsewa,”

Inji ministan

Mafita kan matsalar wuta a Najeriya

Domin magance wannan, ya ba da shawarar ƙara amfani da makamashi na dabam, musamman tsarin da ba ya dogaro da babban layin wuta na kasa

Ya ƙara da cewa samar da wutar sola da sauran hanyoyin makamashi zai ƙara tabbatar da tsaron makamashi da kuma taimakawa wajen cimma burin kare muhalli.

Legit ta tattauna da Hauwa'u

Yayain da rashin wuta ya kara kamari, wata mata a jihar Gombe, Hauwa'u Muhammad ta bayyana cewa lamura da dama sun tsaya kuma jama'a na kara shan wahala.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani kan jita jitar nada sabon Firayim ministan Isra'ila madadin Netanyahu

"Ko akwai wutan ma ba kowa yake iya sayen katin ba, balle kuma yanzu da babu ita sosai. Ana zafi sosai, mutane suna shan wahala."

Ta kara da cewa:

"Kana cikin daki zafi, ka fita waje zafi. Ko ina babu sauki. Ya kamata su yi gyara gaskiya."

Gargadi kan matsalar wutar lantarki

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan matsalar wutar lantarki da za a iya fuskanta a fadin kasa baki daya.

Hakan na zuwa ne yayin da aka shirya wani gyara na musamman a kan abin da ya shafi iskar gas da masu samar da wuta ke amfani da shi.

Hukumar NISO mai alhakin lura da wutar lantarki a Najeriya ta fitar da wani tsari da ta ce idan aka bi za a samu saukin matsalar wuta a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng