Yakin Amurka, Isra'ila da Iran Ya Taba Najeriya, Farashin Litar Fetur Ya Haura N1350
- Litar man fetur ta kusa kai ₦1,400 a sassan Najeriya sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya saboda rikicin Amurka, Isra'ila da Iran
- Direbobin motocin kasuwa a Legas da Kano sun koka kan yadda yanzu ba sa samun riba, yayin da matafiya ke fama da tsadar kudin sufuri a kasar
- Wasu da aka zanta da su, sun bayyana irin radadin da suke ji game da wannan karin kudin, wanda ake fargabar zai ci gaba da tashi a nan gaba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ci gaba da tashin farashin man fetur ya ƙara tsananta radadin tattalin arziki a faɗin Najeriya, inda a yanzu farashin lita ɗaya ya kusa kai ₦1,400 a wurare da dama.
Wannan lamari ya jefa direbobi, matafiya, da masu sana'o'i cikin fargaba sakamakon yadda farashin danyen mai a kasuwar duniya yake tashi.

Kara karanta wannan
Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Source: Getty Images
Farashin litar fetur ta kai kusan ₦1,400
Binciken jaridar Daily Trust a manyan birane ya nuna cewa wannan ƙarin ya samo asali ne daga tashin farashin danyen mai da ya kusa kai $120 a kowace ganga a makon jiya, kafin ya tsaya a kan $112 sakamakon yaƙin Amurka, Isra'ila da Iran.
Wannan ya sa matatar Dangote ma ta ƙara farashin dake fita daga matatar daga ₦1,175 zuwa ₦1,245 a kan kowace lita. Sakamakon haka, masu gidajen mai sun sauya farashinsu zuwa tsakanin ₦1,310 zuwa ₦1,400.
A birnin Legas, direbobin motocin kasuwa sun koka kan yadda ribarsu ke raguwa, inda gidajen mai na NNPCL ma suka ƙara farashi har sau biyu a cikin kwanaki kaɗan.
Toheeb Sulaimon, wani direban mota, ya ce samunsa na kullum ya ragu sosai; inda a baya yake kashe ₦9,000 wajen sayen mai, yanzu yana kashe sama da ₦20,000.
Farashin fetur a Arewacin Najeriya
A birnin Kano kuwa, farashin ya haura zuwa ₦1,390 a gidajen mai na masu zaman kansu kamar AA Rano. Wannan ya sa 'yan acaba da masu keke-napep ƙara kuɗin zirga zirgarsu.
Wani mazaunin garin Kano, Ismail Mabo, ya bayyana cewa an caje shi ₦4,000 kan tafiyar da a baya ake yin ta a kan ₦1,000.
Legit Hausa ta samu labari cewa wasu matafiya sun saye litar man fetur a kan N1, 300 a safiyar ranar Lahadi, sai dai da alama farashin yana ta kara tashi a yanzu.
A birnin Abuja ma, farashin ya tashi zuwa tsakanin ₦1,361 da ₦1,370 bayan sabon tsarin farashi da kamfanin MRS Oil ya fitar.
A jihar Kwara ma, musamman a Ilorin, ana sayen litar fetur tsakanin ₦1,295 zuwa ₦1,343. Wata ma'aikaciyar gwamnati, Oladuni Lateefat, ta bayyana cewa albashinsu ba ya iya biyan buƙatun sufuri da na gida a yanzu, kuma tana tunanin ajiye motarta.

Source: Getty Images
Direbobin mota sun hakura da aiki
Wani mai mota, Mista Fidelis Nte, ya bayyana wa jaridar Nigerian Tribune a jiya Lahadi cewa ya daina fita aiki da motarsa yanzu.
A cewarsa, daga babban yankin Legas (Mainland) zuwa Victoria Island, yanzu tana cinye masa ₦20,700 a kowace tafiya ɗaya, maimakon ₦12,900 da yake kashewa a farkon watan Fabrairu lokacin da lita take ₦860.
Shi ma wani mai motar, Ayo Adebisi, ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da sayen litar mai 10 a kowace rana ba, wanda yanzu farashin litar ya tashi zuwa tsakanin ₦1,360 da ₦1,380.
Yakin Iran: Dangote ya kara kuɗin fetur
Tun da fari, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta kara farashin man fetur da take sayarwa abokan huldarta da ₦70, wanda ke nufin lita daya yanzu ta koma ₦1245.
Sabon farashin zai fara aiki ne daga karfe 12:00 na daren yau Asabar, kuma zai shafi har da man da aka biya kudinsa amma ba a dauka ba.
An dora alhakin wannan karin kudin a kan tashin hankalin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya wanda ya shafi farashin danyen mai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

