Zambar N90.4m: Kotu za Ta Sanar Da Makomar Hujjojin EFCC kan Tsohon Shugaban NHIS
- Kotu ta karɓi ƙarin takardu a shari’ar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ce ta maka shi a gaban kotu tana tuhumarsa da wawure N90.4m
- Sababbin takardun, wadanda karin hujjoji ne a zargin da EFCC ta yi zai iya taimaka mata wajen tabbatar da zargin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babbar kotun birnin tarayya da ke Kuchiako, Kuje a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Chinyere E. Nwecheonwu, taci gana da zama a kan shariar Farfesa Usman Yusuf.
Ta amince da ƙarin takardu da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar a matsayin hujja a shari’ar da ake yi wa tsohon Shugaban hukumar inshorar lafiya, Farfesa Usman Yusuf.

Source: Twitter
A sakon da EFCC ta wallafa a shafin Facebook ta ce a zaman kotun na ranar Laraba, 25 ga Fabrairu, 2026, lauyan gwamnati, Francis Usani, ya roƙi kotu ta karɓi takardun.
An ci gaba da shari'ar tsohon Shugaban NHIS
Hukumar EFCC ta gabatar da takardun a ranar 5 ga Janairu, 2026. Shaidan gwamnati na biyu, James Balami, darakta a hukumar NHIS, shi ne ya gabatar da takardun a gaban kotu.
Mai Shari’a Nwecheonwu ta yanke hukuncin cewa an gabatar da takardun ne bisa ƙa’ida da doka ta tanada, tare da lura da cewa lauyan wanda ake ƙara, O.I. Habeeb, SAN bai kalubalanci hakan ba.

Source: Twitter
Daga cikin takardun da kotu ta amince da su akwai kwafen wasiƙu masu ingantaccen shaida (CTC) na ranar 11 ga Nuwamba, 2016.
An sanya wa takardun alamar E1 zuwa E32. Haka kuma, an karɓi tsarin sayayya na NHIS na shekarar 2016 mai alamar F1 zuwa F4, da na shekarar 2017 mai alamar G1 zuwa G5, sai kuma dokar sayayya ta NHIS ta 2016 mai alamar H1 zuwa H2.
An dage shari'ar tsohon Shugaban NHIS
A ci gaba da shari’ar, an jagoranci shaida na biyu wajen bayar da shaida kan yadda aka gayyace shi zuwa ofishin EFCC da kuma irin bayanan da ya bayar.
Ya shaida wa kotu cewa bayan ya kai takardun da ake bukata, ya rubuta bayanai da dama ga hukumar.
Sai dai yunƙurin mai gabatar da ƙara na shigar da waɗannan bayanai na wajen kotu a matsayin hujja ya fuskanci turjiya daga lauyan wanda ake tuhuma.
Lauyan wanda ake ƙara ya nuna adawa da amincewa da bayanan, lamarin da ya sa aka shiga muhawara tsakanin ɓangarorin biyu kan sahihancin shigar da su cikin hujjojin shari’ar.
Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin, Mai Shari’a Nwecheonwu ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranakun 13 da 14 ga Mayu, 2026, domin yanke hukunci kan ko za a amince da bayanan.
Hukumar EFCC na tuhumar Farfesa Yusuf da laifuffuka biyar da suka haɗa da almundahana da kuma damfara da ta kai N90,439,178.00.
Tsohon Shugaban NHIS ya gamu da cikas
A baya kun ji cewa tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf zai ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta ƙi amincewa da buƙatar neman belin da tsohon shugaban na hukumar NHIS ya gabatar gabanta.
Alƙalin kotun ya ƙi amincewa da buƙatar belin ne saboda hukumar EFCC na son yin gyare-gyarenlna tuhume-tuhumen da take yi masa na almundahana.
Asali: Legit.ng


