Kisan Masu Sallar Tarawihi a Masallaci Ya Tayar da Hankali, ana Ta Magana

Kisan Masu Sallar Tarawihi a Masallaci Ya Tayar da Hankali, ana Ta Magana

  • 'Yan Najeriya sun fara Allah wadai game da wani hari da 'yan ta'addan Lakurawa suka kai kan al'ummar Musulmi suna sallah a Kebbi
  • Masu tsokaci sun nuna takaici game da harin 'yan ta'addan musamman lura da cewa lamarin ya faru ne a watan Ramadan ana sallah
  • Hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa harin abin Allah wadai ne, inda ya yi kira ga gwamnati da dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Kai hari masallaci ana sallar tarawihi a jihar Kebbi ya tayar da hankali a Najeriya, inda jama'a suka fara Allah wadai.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ramuyar gayya ne kan fararen hula bayan ragargazar da dakarun Najeriya suka musu a baya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Lakurawa sun bude wuta a masallaci, sun kashe mutane ana sallar tarawihi

Masallacain Kebbi da aka kai hari
Cikin masallacin da Lakurawa suka kai hari. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, hadimin tsohon Shugaban kasa Bashir Ahmad ya bukaci a dauki mataki wajen kawo karshen irin hare-haren.

Kiran Bashir kan hari a masallaci

A bayanin da ya yi, Bashir Ahmad ya bayyana cewa tsantsar rashin imani ke a kai harin kan mutane na tsaka da ibada a watan Ramadan.

Ya ce:

"Hare-haren da ‘yan ta’addan Lakurawa ke ci gaba da kai wa kan fararen hula marasa laifi suna matukar tayar da hankali kuma ba za a amince da su ba.
"Sun kai hari wani masallaci a daren jiya a Jihar Kebbi tare da kashe masu ibada a wannan wata mai alfarma na Ramadan."

Yayin da ya yi magana kan daukar mataki, Bashir ya ce:

"Dole ne kowa ya yi Allah-wadai da irin wadannan hare-hare marasa ma’ana, sannan hukumomi su dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da maido da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan Boko Haram sun farmaki karamar hukumar gwamna ana cikin Ramadan

Martanin sauran 'yan Najeriya

A karkshin rubutun da Bashir Ahmad ya yi a Facebook, mutane sun bayyana ra'ayoyi daban-daban da ke Allah wadai da harin da aka kai masallacin.

Muhammad Maigari ya ce:

"Ban san ko ku na jin dadi ne da saka labaran kashe-kashe ba. Ku na ganin muna farin ciki da ganin irin wadannan rubuce-rubuce?
"Idan har sakonninku na kai wa inda ya dace, da tuni gwamnati ta dauki wani mataki a kai. Ko kuma ku rika bayar da shawarwari kan mafita, ko ku yi addu’a. Allah Ya kawo karshen wannan kashe-kashen. Amin ya Allah."

Ahmad Sani Abdussalam ya bukaci sanar da gwamnati maimakon rubutu a intanet:

"Ku rika yi wa mutanen da abin ya shafa bayani don Allah"

Abba Bichi ya yi korafi da cewa kullum ana magana idan an kai hari amma ba a daukar mataki:

"Ameen, amma wannan shi ne abin da muke fada a kullum idan irin haka ta faru."

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: 'Yan bindiga sun sake tafka ta'addanci ana cikin azumi a Zamfara

Musa Abubakar ya bayyana cewa:

"Allah-wadai kadai bai isa ba. Idan shugaban ku ba zai iya ba mu tsaro ba, ya kamata ya sauka."

Isiyaku Garba Bala ya bukaci a yi bincike:

"Ya kamata a fara bincike na karkashin kasa kan kashe-kashen da ake yawan samu a Arewacin Najeriya, musamman a masallatai."

Sojoji sun kashe Boko Haram

A wani labarin, mun kawo muku cewa Dakarun Najeriya sun gwabza fada da 'yan ta'addan Boko Haram a wani kauye na jihar Borno.

Wani jami'in sojan Najeriya ya tabbatar da kashe 'yan Boko Haram takwas, raunata wasu daga dama kafin wasu su tsere su koma cikin daji.

Baya ga kashe 'yan ta'addan, wata majiya daga rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa an kwato makamai da suka hada da bindigogi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng