Sanusi II Ya Haska Matsalolin da Ke Sa Iyaye Yi Wa Yara Auren Wuri a Arewa
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tabo batun yi wa yara auren wuri a wasu sassan yankin Arewacin Najeriya
- Muhammadu Sanusi II ya danganta matsalar da gazawar gwamnati wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yin abin da ya dace
- Sarkin ya nuna cewa ana yin watsi da ainihin dalilan da ke tursasa iyaye kai yaransu zuwa gidan miji duk da suna da kananan shekaru
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan matsalar yi wa yara auren wuri a Arewacin Najeriya.
Sanusi II ya danganta ci gaba da aurar da yara da wuri a wasu sassan Arewacin Najeriya da gazawar gwamnati wajen samar da isassun makarantu da tsare-tsaren rayuwa ga ’yan mata bayan kammala makarantar firamare.

Source: Facebook
Sanusi II ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da da aka yi da shi a shirin 'The Morning Brief' na tashar Channels TV.
Ya gudanar da hirar ne tare da Obi na Onitsa, Nnaemeka Alfred Achebe da Sarkin Shonga, Haliru Yahaya Ndanusa, inda suka tattauna kan al’adu, ilimi da gyaran zamantakewa.
Me Sanusi II ya ce kan auren wuri?
Sarkin ya ce duk da cewa ana yawan mayar da hankali kan batun aurar da yara da wuri a bainar jama’a, ana yin watsi da ainihin dalilan da ke tilasta iyalai ɗaukar irin waɗannan matakai.
Ya ce yawancin ’yan mata kan kammala firamare suna da kananan shekaru, amma ba su da wata hanya ta ci gaba da karatu ko koyon sana’a.
"Babu makarantar sakandare, babu cibiyar koyon sana’a, babu wani tsari da aka tanadarwa mace don rayuwarta.”
- Muhammadu Sanusi II
Halin da iyaye suka tsinci kansu a ciki
A cewarsa, a irin wannan hali, iyaye talakawa ba al’ada ce ke tursasa musu ba, tsoro ne ke sa su aurar da ’ya’yansu mata tun da wuri.
“Muna magana ne kan auren wuri ga yara, amma idan ka je wasu sassan Arewa, makarantar firamare ce kawai suke da ita, shi ke nan."
“Daga shekara 11 zuwa 18, wane tsari ka tanadat mata? Talakan mutum yana ganin yarinya ta kai shekara 12 ko 13, yana tsoron kada ta yi ciki a hanya, sai duk wani saurayi da ya zo ya aurar da ita. Wani lokaci waɗannan al’adu suna nuna talauci ne kawai.”
- Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi II ya soki 'yan birni
Sarkin ya soki ra’ayoyin mutanen da ke rayuwa a birane da ke yin watsi da halin da ake ciki a karkara, yana mai cewa hanyoyi ba su da tsaro, makarantu suna nesa ko ma babu su gaba ɗaya.
"Abu ne mai sauƙi a zargi al’ada. Abu ne mai sauƙi a zargi wanda aka cutar. Amma gwamnati ba ta samar da makarantu ba.”
Sanusi ya ƙara da cewa, bisa ga kundin tsarin mulki, kowane yaro yana da ’yancin samun ilimi. “Don haka idan ka cire yaro daga makaranta, a ka’ida ka aikata laifi."
- Muhammadu Sanusi II

Source: Facebook
Sanusi II ya nuna yatsa ga gwamnati
Sai dai Sarkin na Kano ya yi tambaya kan yadda za a aiwatar da dokar alhali ita kanta gwamnati ta gagara cika nauyin da ke kanta.
“Amma mutane nawa aka taɓa kamawa saboda sun cire yaro daga makaranta? Babu ko ɗaya."
- Muhammadu Sanusi II
Khalifa Sanusi II ya gargadi masu dukan mata
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya aika da sakon gargadi ga maza masu dukan matansu.
Mai martaba Sanusi II ya ce ba daidai ba ne namiji ya dinga dukan mace ko cin zarafinta saboda hujjar cewa al’ada ta ba shi dama.
Ya jaddada cewa mata ‘yan ƙasa ne na Najeriya, kuma doka ta tanadi kariya gare su kamar kowa da ke rayuwa a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


