Zargin Ta'addanci: DSS Ta Gurfanar da Abubakar Malami da Yaronsa a gaban Kotu

Zargin Ta'addanci: DSS Ta Gurfanar da Abubakar Malami da Yaronsa a gaban Kotu

  • Hukumar DSS ta gurfanar da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, da ɗansa kan zargin ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba
  • Abubakar Malami SAN da ɗansa sun musanta zargin da aka gabatar masu tare da cewa zargin ba shi da tushe
  • Kotun ta umarci a tsare su a hannun DSS har zuwa ranar 20 ga Fabrairu domin fara shari’a a kan zarge-zargen

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – A ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2026, Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS) ta gurfanar da tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, da ɗansa Abdulaziz, a kotu.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Hukumar DSS ta maka su gaban Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhuma biyar da suka shafi ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ana zargin Abubakar Malami da dansa da goyon bayan ta'addanci
Abubakar Malami SAN, tsohon Ministan shari'a na Najeriya Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa a cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CR/63/2026, ana zargin Malami da wasu da ake tuhuma a shari’ar da tallafa wa ‘yan ta’adda yayin da ya ke Minista a Ma’aikatar Shari’a.

Zargin da DSS ke yi wa Abubakar Malami

Jaridar The Nation ta wallafa cewa haka kuma, an zargi Malami da ɗansa da ajiyar makamai a gidansu na Gesse Phase II, Birnin Kebbi, ba tare da izini ba.

DSS ta bayyana cewa a ƙarar farko, Malami ya yi laifin goyon bayan kudin ta’addanci, yayin da Malami da ɗansa suke fuskantar zargi a ƙididdiga na biyu zuwa biyar kan mallakar bindiga Sturm Magnum 17-0101.

Kara karanta wannan

Bayan jirgi marar matuki ya hallaka sojoji, rundunar ta fadi matakin da ta dauka

An ci gaba da tsare Malami har zuwa 20 ga watan Fabarairu, 2026
Abubakar Malami SAN da wasu daga cikin jami'an DSS Hoton: Abubakar Malami SAN/DSS Unofficial
Source: Twitter

Haka kuma ana zargin ya mallaki harsasai 16 na Redstar AAA 5720, da harsasai 27 da aka harba, wanda sabawa doka ce karkashin dokar yaki da ta'addanci da makamai na sharar 2022 da 2004.

Malami da ɗansa sun musanta dukkannin tuhume-tuhumen lokacin da aka karanta masu abin da ake zargin su da aikata wa.

Kotu ta garkame Malami da ɗansa

Bayan sun musanta zargin, lauyan mai kara Calistus Eze ya roƙi kotu ta tsare su a hannun DSS har sai an fara shari’a amma lauya su, Shuaibu Aruwan (SAN), ya nema a baki a ba su beli, yana mai cewa sun jima a hannun DSS fiye da makonni biyu.

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Amma Alkali Joyce Abdulmalik ta ƙi bayar da beli, kuma ta umarci lauyan su Malami da ya shigar da takardar neman beli a hukumance.

Kotun ta umarci a tsare Malami da ɗansa a hannun DSS har zuwa ranar 20 ga Fabrairu, 2026 ranar da za a fara shari’a.

Tuhumar da aka gabatar sun haɗa da: ta’addanci da tallafa wa masu laifi, mallakar bindiga da harsasai ba tare da izini ba, da shiri yin ta’addanci a gidansu da ke Birnin Kebbi.

Kotu ta kwace kadarorin Abubakar Malami

A baya, kun ji cewa Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da (AGF), Abubakar Malami, SAN.

Hukumar EFCC ce ta shigar da bukatar kwace kadarorin bisa zargin cewa Malami, tsohon ministan shari'a ya mallake su ta hanyar amfani da kudin haram.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, shugabannin jam'iyya sun zauna, an tsayar da lokacin babban taron APC

ARA Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, yayin da yake yanke hukunci kan wata buƙatar gaggawa da hukumar EFCC ta shigar gabanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng