Kano Ta Yi Zarra, Ta Doke Jihohi sama da 30 wajen Inganta Yanayi
- Jihar Kano ta tashi daga matsayi na 35 zuwa matsayi na huɗu a fannin kula da sauyin yanayi a Najeriya
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu yabo kan jagoranci da gyaran tsare-tsare na hukumomi da ci gaba da inganta muhalli
- Ma’aikatar Muhalli a jihar ta bayyana cewa ba a nan gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta tsaya ba, akwai wasu shirye-shiryen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahiru Hashim, ya bayyana cewa jihar ta samu gagarumin cigaba a ma’aunin kula da sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa a halin yanzu a Najeriya, Kano ta tashi daga matsayi na 35 zuwa matsayi na huɗu cikin shekara guda.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wa bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kano yayin wani taro da aka shirya domin cika shekara guda da hawansa ofis.
Jihar Kano ta samu ci gaba
The Cable ta ruwaito cewa Dr. Dahiru Hashim ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga jagoranci mai hangen nesa, gyare-gyaren hukumomi a Jihar.
Ya kuma ce an samu haɗin gwiwa mai ɗorewa tsakanin hukumomin gwamnati da abokan hulɗar ci gaban harkokin yanayi.
Kwamishinan ya bayyana cewa a shekarar 2024, Kano na cikin jihohin da suka fi fuskantar matsaloli, inda aka sanya ta ta 35 cikin jihohi 36 na ƙasar nan.
A cewarsa:
“A wancan lokaci, wannan matsayi abin damuwa. Ban san cewa nan ba da jimawa ba zan samu damar taka rawa wajen sauya wannan labari ba.”
Ya ƙara da cewa matsayi na huɗu da Kano ta samu a yanzu hujja ce cewa idan aka samar da ingantattun tsare-tsare da haɗin kai a harkokin mulki, ana iya cimma sakamako mai kyau.
An yabi gwamnatin jihar Kano
Kwamishinan ya jaddada cewa wannan nasara ba ta ofishi ko mutum guda ba ce, illa sakamakon yadda aka bar hukumomi su yi aikinsu yadda ya dace.
Ya ce gwamnatin Kano na da aniyar ƙarfafa wannan cigaba tare da neman kaiwa matsayi na ɗaya a zagayen tantancewar kula da sauyin yanayi na gaba.
Dahiru Hashim ya danganta wannan cigaba da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ba wa bangaren fifiko.
Ya bayyana cewa jagorancin gwamnan ya dawo da tsari da daidaito a hukumomi, tare da ƙarfafa mulki da suka ginu kan cancanta, gaskiya da ɗaukar alhaki.

Source: Facebook
A cikin shekara guda da ta wuce, Dakta Dahiru Hashim ya ce ma’aikatar ta mai da hankali kan dawo da ingantattun tsare-tsare, ƙarfafa haɗin gwiwa a bangaren muhalli.
Ya kara da cewa sun mayar da hankali a kan tsaftar muhalli, rage ambaliya, magance zaizayar ƙasa, samar da ruwan sha, dashen itatuwa da tsara manufofin sauyin yanayi.
Kwamishinan ya yaba wa ma’aikatan ma’aikatar da hukumominta bisa jajircewarsu, yana mai cewa gudunmawarsu ta kasance ginshiƙi wajen nasarorin da aka samu.
Haka kuma ya gode wa abokan hulɗar ci gaba, ciki har da Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya (FCDO) ta hanyar shirin PACE, UNICEF da sauran su.
Kano ta dauki kambu tsakanin jihohi
A baya, mun wallafa cewa Kano ta samu babban cigaba a fannin tattara kuɗin shiga, inda ta ninka abin da take samu da sama da kashi 100 a daidai lokacin da jihohi ke fama da kalubale.
Wannan na ƙunshe cikin wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar, tare da tabbatar wa daga Statista, babbar cibiyar tattara bayanai a Najeriya kan batun kididdiga.
Rahoton ya nuna cewa Kano ta kasance cikin jihohin da suka fi nuna ƙwazo wajen inganta hanyoyin samun kuɗin shiga, lamarin da ya ɗaga darajarta a matakin ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


