Daga Chibok, Kankara zuwa Maga: Dubban Dalibai da Aka Sace tun daga 2014 a Arewa

Daga Chibok, Kankara zuwa Maga: Dubban Dalibai da Aka Sace tun daga 2014 a Arewa

Rahotanni sun nuna hare-haren ’yan bindiga sun shafi dubban dalibai cikin shekaru 11 da wanda ya tayar da hankula musamman sace-sacen Niger da Kebbi wanda suka tunzura jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sababbin hare-haren makarantun Niger da Kebbi sun haifar da tsoro a tsakanin dalibai da iyayen yara.

A makon jiya, yan bindiga suka dauke dalibai 303 daga makarantar cocin Katolika a Niger; kwana biyar kacal bayan sace dalibai 25 a Jihar Kebbi.

Yawan dalibai da aka sace a Arewacin Najeriya
Hafsan sojojin Najeriya tare da dakarunsa a Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Jerin sace-sacen dalibai a Arewa daga 2014

Rahoton Vanguard ya tabbatar da hare-haren makarantu akalla 22 daga 2023 zuwa 2025, inda aka sace dalibai 816, baya ga wadanda ba a ruwaito ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan hare-haren sun daɗe suna faruwa tun 2014 lokacin da Boko Haram ta sace ’yan mata 276 na Chibok, lamarin da ya girgiza duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

An fitar da cikakken jerin sunayen malamai da daliban da aka sace a jihar Neja

Save the Children da UNICEF sun ce an kai hare-hare 70 daga 2014 zuwa 2022, inda aka sace dalibai sama da 1,680 kuma aka kashe yara fiye da 180 yayin da zuwa 2025 an sace dalibai 2,496.

1. Daliban da aka sace a Borno da Yobe

I. A ranar 14 ga watan Afrilun 2014, yan Boko Haram sun sace dalibai 276 daga makarantar mata ta gwamnati a karamar hukumar Chibok da ke Jihar Borno.

Sace wadannan yan mata ya tayar da hankulan al'umma, gwamnati wanda ya jawo hankalin mutanen duniya da kiran a yi gaggawar dawo da su cikin koshin lafiya.

II. Har ila yau, bayan shekaru hudu da sace daliban Chibok a jihar Borno wanda ya jawo hankalin duniya, an dauke wasu a Yobe.

A ranar 19 ga Fabrairun 2018, an sace dalibai 110 daga kwalejin kimiyya da fasaha ta mata da ke Dapchi, Jihar Yobe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tun a 2014 Boko Haram suka sace yan matan Chibok
Shugaba Bola Tinubu da wasu daga cikin yan matan Chibok. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

2. An sace dalibai a Sokoto, Plateau

I. Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari a Plateau inda suka sace daliban Jami'ar Jos bakwai a ranar 14 ga Yuni 2023.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta yi magana kan sace dalibai a Kebbi da Neja

II. A Sokoto kuma, a ranar 9 Maris 2024, yan bindiga sun sace dalibai 15 na makarantar Tsangaya a Gidan Bakuso a karamar hukumar Gada a Sokoto.

3. An sace daliban GSSS Kankara a Katsina

I. Hankula sun tashin yayin da yan bindiga suka kai farmaki a makaranar kimiyya da fasaha a karamar hukumar Kankara.

Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Disamba 2020 inda aka yi awon gaba da sama da yara 300 ba tare da samun turjiya daga jami'an tsaro ba.

II. Majiyoyi sun tabbatar da sace wasu dalibai a jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina mai fama da matsalar tsaro.

Maharan sun kai farmakin ne a ranar 4 ga watan Oktoba 2023 inda suka yi nasarar dauke dalibai har guda biyar.

An sace dalibai da dama a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke iyaka da Nijar. Hoto: Legit.
Source: Original

4. Dalibai da aka sace a Kaduna

I. A ranar 11 Maris 2021 an sace dalibai 39 ( mata 23 da maza 16) daga kwalejin tarayya ta gandun daji a Afaka da ke jihar Kaduna.

II. Har ila yau, a ranar 20 ga watan Afrilun 2021 an sace akalla dalibai 20 daga jami'ar Greenfield da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Neja: Wasu dalibai da aka sace sun yi dabara, sun gudo daga hannun 'yan bindiga

III. Wasu yan bindiga sun kutsa makarantar coci ta Bethel Baptist a ranar 5 ga Yuli 2021 inda suka sace sama da dalibai 120 a Chikun da ke Kaduna.

IV. Bugu da kari, a ranar 3 ga Afrilun 2023 yan bindiga sun sace dalibai takwas na makarantar gwamnati da ke Awon a karamar hukumar Kachia a Kaduna.

V. A ranar 4 ga watan Afrilun 2023, yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 10 a makarantar gwamnti a jihar Kaduna.

VI. Majiyoyi sun tabbatar da cewa a ranar 24 ga Agustan 2023 an kai hari makaranta a Chikun a Kaduna inda aka kashe mutum 1, an sace dalibai bakwai da malami daya.

VII. Wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a makarantar firamare da ke Kuriga a jihar Kaduna a ranar 7 ga Maris 2024 inda suka sace dalibai 287.

5. Daliban da aka sace a Zamfara

I. Yan bindiga a ranar 26 ga Fabrairun 2021 sun kai hari a makarantar mata ta gwamnati da ke Jangebe a Zamfara inda suka dauke dalibai 279.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

II. Bayan shekaru biyu da sace dalibai a Jangebe, miyagu sun kuma kai hari a Bungudu da ke jihar a ranar 2 ga Afrilun 2023 inda suka dalibai biyu

III. Har ila yau, a ranar 8 ga Afrilun 2023, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sama da yara masu shekaru 12–17 guda 80 a karamar hukumar Tsafe da ke Zamfara.

IV. Yan bindiga dauke da makamai a ranar 22 ga Satumbar 2023 sun kuma kai hari jihar, sun sace yan mata 24 daga dakunan kwanan mata na jami'ar tarayya da ke Gusau a Zamfara.

6. Yawan daliban da aka dauke a Nasarawa

I. A ranar 20 ga watan Janairun 2023 al'umma sun shiga zullumi bayan kai hari a makarantar firamare ta LGEA a Nasarawa inda aka yi garkuwa da dalibai shida da safe.

II.Har ila yau, a ranar da aka sace dalibai shida a makarantar, an kuma dauke wasu dalibai shida a Doma, Jihar Nasarawa.

III. Sannan a ranar 26 ga Satumba 2023, an sace ɗalibi daga kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai a birnin Lafia da ke jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

IV. Har ila yau, wasu yan bindiga sun farmaki wasu dalibai a jami'ar Nasarawa inda suka yi nasarar dauke mutum hudu a ranar 10 ga Oktoba 2023.

An sace dalibai masu tarun yawa a Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa da yan bindiga suka sace dalibai da yawa. Hoto: Legit.
Source: Original

7. An sace dalibai a Kebbi

I. Jihar Kebbi na daga cikin jihohi da ke fuskantar matsalolin harin yan bindiga, a ranar 17 ga Yuni 2021, an sace kusan dalibai 11 a Yauri da ke Jihar Kebbi.

II. Wanda ya fi daukar hankali a kwanan nan shi ne daliban da aka sace a ranar 17 ga Nuwamba 2025 inda maharan suka dauke dalibai 25 daga makarantar mata da ke Maga a Kebbi.

8. Yawan dalibai da aka sace Niger

I. Tun a ranar 17 ga Fabrairu 2021, miyagu sun kai hari kwalejin kimiyya da ke Kagara a Niger inda suka sace dalibai 27 da wasu ma’aikata.

II. Bayan wata uku, wasu yan bindiga sun kuma kai farmaki a makarantar Islamiyya a Tegina da ke jihar inda suka sace dalibai 200 a watan Mayun 2021.

III. Sannan a ranar 25 ga watan Maris din shekarar 2023 yan bindiga suce yara biyu a karamar hukumar Suleja da ke Jihar Niger, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

CAN: Dalibai da malamai 227 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a Jihar Neja

IV. Har ila yau, a ranar 21 ga Nuwamba 2025, yan ta’adda sun kai hari makarantar Katolika a Papiri da ke Jihar Niger inda suka sace dalibai 303.

An sace dalibai da dama a makarantar coci a Nigeri
Hoton babban kofar shiga makarantar Katolika da aka kai hari a Neja Hoto: John Ayuba.
Source: Facebook

Dalibai 25: Gwamnatin Kebbi ta gano kuskuren sojoji

Kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi ya sake nuna damuwarsa kan yadda sojoji suka janye kafin sace dalibai mata a makarantar GGCSS Maga.

Nasir Idris ya yi kiran da a binciki dalilin da ya sanya aka janye dakarun sojojin 'yan mintuna kadan kafin 'yan bindiga su kawo harin.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa da sun san za a janye sojojin da sun rufe makarantar domin hana aukuwar harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.