Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata sama da 200 a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata sama da 200 a jihar Zamfara

- Karo na uku, tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da daliban makarantan kwana a Najeriya

- Wannan na zuwa mako guda bayan awon gaba da dalibai maza a jihar Neja

- Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da garkuwa da yaran

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa yan bindiga sun sace daliban makaranta mata a jihar Zamfara.

Majiyoyin Legit Hausa sun tabbatar da ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata wanda ba'a san ainihin adadinsu ba har yanzu daga makarantar sakandiren GSS Jengebe, karamar hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara.

Majiyoyin sunce an sace wadannan dalibai ne misalin karfe daya na dare.

Wasu yan asalin garin biyu sun bayyana cewa anyi awon gaba da kannensu mata.

Faisal Jangebe yace: "Ya Allah kayima kannenmu mafita jama.a munaneman addu.arku akan wannan matsala dake addabarmu."

Hakazalika, Isma'il Lawali Jangebe yace: "Wannan labarin Gaskiya ne, a kauyenmu akayi, Dafatar Allah ya masu mafita."

DUBA NAN: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata kimanin 300 a jihar Zamfara
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai mata kimanin 300 a jihar Zamfara
Asali: Original

DUBA NAN: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

Hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta'addanci ko kuma tayi murabus.

A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar 'yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen 'yan ta'adda ko tayi murabus.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel