An hango 'yan karin wasu 'yan matan Chibok 6 a dajin Sambisa
Iyayen 'yan matan Chibok, da mayakan kungiyar Boko Haram su ka sace tun shekarar 2014, sun ce 'yan matan 6 ne kawai aka hango a dajin Sambisa ba 57 ba kamar yadda rahotanni wasu kafafen ke yadawa.
Mai magana da yawun iyayen 'yan matan Chibok da aka sace, Mista Ayuba Alamson, ya shaidawa manema labarai a Maiduguri cewar wata mata ce da ta kubuto daga hannun mayakan Boko Haram ta tabbatar ma su da cewar ta zauna tare ne da 'yammata 6 kacal.
Alamson, ya ce yarinyar da ta kubuto daga hnnun mayakan na Boko Haram a dajin Sambisa sunan ta Jummai Abouku, kum tuni jami'an soji su ka mika ta hannun iyayenta bayan tantance ta.
A cewar Alamson, "Mayakan kungiyar Boko Haram sun sace Jummai, uwar 'ya'ya 6, tare da babban yaron ta a Askira Uba tun shekarar 2014."
Alamson ya kara da cewar Jummai ce ta shaida ma su cewar ta zauna ne tare da 'yan matan makarantar Chibok 6 yayin da ta ke hannun 'yan Boko Haram a dajin Sambisa. Kazalika ya ce tuni ta sanar da iyayen 'yan matan 6 da su ka zauna tare.
"Jummai ta shaida mana cewar 'yan matan 6 na auren mayakan kungiyar Boko Haram ne, daya a cikinsu na da juna biyu bayan haihuwar da namiji a baya, daya na dauke da jariri sai kuma ragowar hudu da har yanzu basu taba haihuwa ba.
"Wasu 'yan watanni kadan kafin ta kubuto, Jummai ta samu juna biyu bayan mayakan sun tilasta ma taauren daya daga cikinsu.
DUBA WANNAN: Wasiyya mai ratsa jiki da Gaddafi ya yiwa 'ya'yansa mata a kashe shi
"Ta samu dmar guduwa tare da yaronta da aka sace su tare kuma ta shafe wani lokaci a sansanin 'yan gudun hijira da ke Bama kafin daga baya a sada ta da iyayenta a Chibok.
"Wannan shine abin da Jummai ta fada mana amma sai mu ka ji wasu kafafen yada labarai na cewa wai an ga kimanin ragowar 'yan matan Chibok 57 a kasar Kamaru," in ji Alamson.
Daga karshe Alamson ya yi godiya ga gwamnatin tarayya bisa kokarinta na dawo da 'yan matan Chibok 100 tare da rokon su rubanya kokarinsu domin ganin ragowar 'yan matan sun samu dawowa gidajen iyayensu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng