Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili

Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili

- Kungiyar Boko Haram ta sanar da daukan alhakin kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara

- A ranar Litinin ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da cewa wadanda suka sace daliban sun tuntubi gwamnati

- Sai dai, a cikin sakon sautin murya da Shekau ya fitar, ya ce basu tuntubi kowa ba dangane da batun sace daliban

Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta sanar da cewa ita ce keda alhakin sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, kamar yadda HumAngle ta rawaito.

A cewar HumAngle, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce har yanzu basu tuntubi kowa dangane da wasu sharuda na sakin daliban ba.

Jaridar ta ce, Shekau ya sanar da hakan ne a cikin wani sakon sautin murya mai tsawon mintuna 4:28 da ya fitar da duku-dukun safiyar ranar Talata.

KARANTA: Sakandire: Dalibai fiye da 500 sun koma makaranta dauke da juna biyu bayan hutun korona

"Abinda ya faru da Katsina ya faru ne domin daukaka addinin Islama da kuma nuna kyamar karatun Boko wanda ilimi ne na turawan yamma da ya saba da koyarwar Allah da manzonsa.

Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a Katsina
Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a Katsina
Source: UGC

"Ba'a koyarwa bisa tsarin Allah da manzonsa a makarantar Boko. Suna rusa addinin Islama. Su na yin hakan ne a sakaye, amma Allah masanin komai ne hatta abinda aka boye. Allah ya daukaka addinin Islama. Allah ya kashemu a matsayin Musulmai," kamar yadda HumAngle ta rawaito cewa Shekau ya fada a cikin sakonsa.

KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

Sannan ya cigaba da cewa, "a takaice, mu ne keda alhakin abinda ya faru a Katsina," ya fada kafin ya gimtse sakon ta hanyar sanar da cewa shine Shekau, shugaban kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal Jihad.

Wannan shine karo na farko da kungiyar Boko Haram ta taba fitowa ta sanar da daukan alhakin kai gagarumin harin sace dalibai a jihohin yankin arewa maso yamma.

A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa Masari ya sanar da shugaba Buhari cewa 'yan bindiga sun tuntubi gwamnatin jiha bayan sun yi awon gaba da daliban makarantar sakandiren Kankara, kamar yadda Channels ta rawaito.

"Gwamnan, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Manir Yakubu, ya ce 'yan bindigar sun kira kuma tuni an fara tattaunawa dasu a kan kiyaye lafiyarsu da kuma dawo da su gidajensu cikin koshin lafiya," kamar yadda Garba Shehu ya sanar a cikin jawabin da ya fitar.

Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun hango wurin da daliban suke tare da bayyana cewa ''akwai alamun samun nasara'' dangane da tattaunawar da aka fara.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel