Mahaifin daya daga cikin daliban Afaka ya mutu sakamakon bugun zuciya
- Allah ya yiwa mahaifin daya daga cikin daliban jihar Kaduna da aka sace ya rasu
- Gwamnatin jihar Kaduna ta gana da iyayen yaran kan halin da ake ciki
- Makonni biyu kenan da sace daliban makarantar Afaka babu labari
Mahaifin daya daga cikin daliban makarantar FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu.
Channels TV ta rahoto cewa Ibrahim, mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.
A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada bayan samun labarin sace diyarsa.
Ya mutu da yammacin Juma'a yayinda yan'uwansa ke kokarin kai shi asibiti.
Labarin mutuwar Ibrahim na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta zanna da wakilan iyayen daliban a gidan gwamnatin jihar.
Yau makonni biyu kenan da sace daliban.
KU DUBA: Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai
DUBA NAN: Zanga Zanga: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Kaduna Sun Bijirewa Umarnin Sojoji
Kun ji cewa malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana game da wasu daliban makarantun gandu ta Kaduna da aka yi garkuwa da su.
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce umarnin da aka ba jami’an tsaro na harbe duk wanda su ka gani ya na dauke da bindigar AK-47 ya sa aka gaza ceto daliban.
Da yake magana da Daily Trust, malamin ya ce ya hadu da wasu ‘yan bindiga da su ka taimaka masa har ya gano gungun wadanda su ka sace wadannan dalibai.
Asali: Legit.ng