An Ceto Yara 2 Cikin Daliban Jihar Nasarawa Da Yan Bindiga Suka Sace

An Ceto Yara 2 Cikin Daliban Jihar Nasarawa Da Yan Bindiga Suka Sace

  • Gamayyar jami'an tsaro a jihar Nasarawa sun kwato dalibai biyu daga hannun yan bindiga a Doma
  • Jami'an yan sanda tare da hadin kai yan kungiyar bijilanti sun shiga daji laluben yan bindigan da suka sace daliban
  • Lamarin yan bindiga masu garkuwa da mutane na cigaba da cin karnukansu ba babbaka a Najeriya

Nasarawa - Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa an samu nasarar ceto dalibai mata biyu cikin daliban makarantar firamaren LEA shida da aka sa ce a garin Alwaza, karamar hukumar Doma.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Rahman Nansel, a ranar Asabar ya bayyana cewa an ceto daliban ne misalin karfe 2:30 na yamma a kauyen Sabon Kwara dake garin Jenkwe na karamar hukumar Obi.

Ya ce sun samu wannan nasara ne a sintirin neman dalibanda jami'an yan sanda tare da hadin kan sauran jami'an tsaro, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

Dalibai
An Ceto Yara 2 Cikin Daliban Jihar Nasarawa Da Yan Bindiga Suka Sace Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Nansel ya ce yanzu haka ana kan hanyar ceto sauran yaran hudu ba tare da sun samu rauni ba kuma an damke wadanda suka sace su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kara da cewa an garzaya da daliban asibiti domin duba lafiyarsu sannan a mikasu ga shugaban karamar hukumar Doma don damkasu ga iyayensu.

Yan bindiga sun sace dalibai 6

A ranar Juma'a, yan bindiga suka kai simame makarantar firamaren LEA na gwamnati suka kwashe wasu daliban makarantar.

Rahotanni sun kawo cewa an kwashe yaran ne da safe lokacin da daliban ke isa makaranta.

Wannan ya shiga jerin harin da yan bindiga zasu kai makarantu a fadin Najeriya.

Yan bindiga sun sace dalibai a Chibok dake Borno, a Dapchi dake Yobe, a birnin Yauri dake Kebbi, a Kagara dake Neja, a Kankara dake jihar Katsina, a garin Afaka dake jihar Kaduna, a Zaria dake Kaduna, Jangebe dake jihar Zamfara, dss.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Sace 'Dalibai 4 A Hanyarsu Na Dawowa Daga Bikin Aure' A Zamfara

Wani mataki gwamnati ta dauka don kare daliban makarantu

Har ila yau, gwamnatin tarayya mai hakkin tabbatar da tsaron rayuwa da dukiyar al'umma bata fitar da wani tsari takamamme na tsaron makarantun gwamnati da na masu zaman kansu ba.

Masana kuma masu sharhi kan lamarin yau da kullum sun bada shawari daban-daban game da yadda gwamnati zata iya bada tsaro a makarantu.

Ra'ayin masana

Tsohon kwamishanan yan sanda kuma masanin lamarin tsaro, Mr. Frank Oditta, ya ce rashin aikin yi ke kawo matsalar garkuwa da mutane.

Ya ce shugabannin makarantu na da gudunmuwar da zasu iya badawa ta hanyar katange makarantunsu da kuma wayar da kan dalibai da malamai kan muhimmancin tsaro.

Yace:

"Abubuwa uku ya wajaba a yi; sanya na'urar CCTV, wayar da kan iyaye da malamai lokacin zaman PTA, sannan ilmantar da dalibi muhimmancin tsaro lokacin tsayuwar taabur."

Asali: Legit.ng

Online view pixel