Yadda 'Yan Bindiga Suka Shiga Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Tarayya Gusau

Yadda 'Yan Bindiga Suka Shiga Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Tarayya Gusau

  • Wasu dalibai sun bayyana hanyoyin da 'yan bindiga suka bi suka shiga ɗakunan kwanan ɗalibai a jami'ar tarayya ta Gusau
  • A wani faifan bidiyo da ake yaɗawa, wani ɗalibi ya ce maharan sun shiga ta Tagogi da Silin suka kwashi dalibai da yawa
  • Wani ɗalibin ajin farko a jami'ar ya shaida wa Legit Hausa cewa 'yan bindiga sun tafi da ɗalibai mata da dama a harin na daren jiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - A safiyar Juma’a ne ‘yan bindiga suka kai farmaki jami’ar tarayya da ke Gusau ta jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai da ba a tantance adadinsu ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun kutsa kai cikin gidan kwanan ɗalibai uku kana daga bisani suka kwashe su, suka yi awon gaba da su.

Kara karanta wannan

Matashin Direban A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m a Kano, Ya Sake Samu Wata Muhimmiyar Kyauta

Tagogin da yan bindiga suka fasa.
Yadda 'Yan Bindiga Suka Shiga Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Tarayya Gusau Hoto: Northern Trending
Asali: Instagram

Dakarun sojin Najeriya sun gwabza musayar wuta da 'yan ta'addan amma duk da haka sai da suka samu nasarar tafiya da ɗaliban zuwa inda ba a sani ba.

Ta ya 'yan bindiga suka iya shiga ɗakunan ɗaliban?

Amma a wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a soshiyal midiya, an ga dalibai da dama suna leka ɗakunan abokan karatunsu ko danginsu da harin ya shafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ji wani dalibi da ba a san ko wanene ba a cikin faifan bidiyon yana cewa ‘yan bindigan sun kutsa cikin dakunan kwanan dalibai ta tagogi da silin.

Ya ce:

"Duka ta taga suka shiga ɗakunan nan, ta tagogin suka fito da ɗaliban, amma ni ban san ɗaƙi mai lamba nawa ne ɗakinta ba, wataƙila wannan ne."

Gilasan tagogi, ƙatako da ragar da aka sanya a jikin tagogin duk an kakkarya su haka nan kuma Katakon da aka buga silin ɗin dakunan da shi duk ya faɗo ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Tare Da Sace Daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Bayanai Sun Fito

Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin da ake fama da matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ‘yan fashin daji suka hana mutane zaman lafiya.

Har yanzun bamu san yawan ɗaliban da aka sace ba in ji ɗalibai

Wani ɗalibin da ke shekarar farko a karatunsa ya shaida wa Legit Hausa cewa babu wasu sojoji da suka kawo ɗauki har sai da yan bindigan suka tafi.

Ɗalibin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda yanayin tsaro ya ce wasu na cewa an sace ɗalibai mata 25, wasu sun ce 40, wasu 50, har yanzun ba a tantance yawansu ba.

"Da misalin ƙarfe 10 aka ce sun shigo ko zasu shigo, to amma wajen ƙarfe 3:00 na dare suka dawo, suka shiga ta tagogi, suka ɗauki ɗalibai mata masu yawa."
"Ba zan iya faɗa maka yawansu ba, amma zaka ji wasu na cewa an sace ɗalibai 20, wasu su ce sama da 30, wasu 50, akwai waɗanda na ji suna cewa an ɗauki ɗalibai kusan 80."

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Jami'an Tsaro da Mutanen Gari Sun Halaka 'Yan Bindiga Sama da 20 a Jihar Arewa

"Abun dai ba daɗi amma ba bu wani jami'in tsaro da ya kawo ɗauki har sai da suka gama abin da suka zo yi, suka tafi, sannan sojoji suka ƙariso."

DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe

A wani labarin kuma Hukumar DSS ta kama mamban majalisar dokokin jihar Ogun da wasu mutum 5 bisa zargin hannu a kashe rayuka sama da 20 a Sagamu.

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa jami'an DSS sun cafke Bello a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai, Akinloye Bankole, ya fitar a Abeokuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel