Jihar Neja: An tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25

Jihar Neja: An tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25

  • Rahotanni sun kawo cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban makarantar Tegina da ke jihar Neja sun raba su zuwa wurare 25 a jeji
  • Mutumin da aka tura don kai kudin fansa ga maharan, Kasimu Barangana ne ya bayyana hakan inda ya koka kan yanayin da ya ga yaran a ciki
  • Ya kuma bayyana cewa maharan sun kewaye yaran sosai don gudun kawo masu hari

Tegina, jihar Neja - ‘Yan makarantar Salihu Tanko Islamiyya da aka sace a Tegina, Jihar Neja, suna tsare a sansanoni 25 a cikin daji, mutumin da aka tura don kai kudin fansa ga maharan ya bayyana.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar 136 a ranar 30 ga Mayu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jihar Neja: An tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25
Mutumin da ya kai kudin fansa ya bayyana cewa an tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An tattaro cewa uku daga cikin daliban sun mutu a hannun wadanda suka sace su a makon da ya gabata.

Kasimu Barangana, mutumin da ya dauki Naira miliyan 30 zuwa wurin barayin, ya ce an ajiye yaran a wurare 25 a cikin jejin da ke dauke da dubban ’yan bindiga masu dauke da makamai.

Kara karanta wannan

A gaskiya Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa

Barangana ya bayyana cewa ‘yan fashin na tsare da yaran sosai inda suke ankare da duk wani motsi a cikin jejin, New Telegraph ta ruwaito.

Masu garkuwan sun kama Barangana a lokacin da ya je kai kudin amma suka sake shi a ranar Litinin bayan ‘yan kwanaki.

Ya bayyana yanayin da yaran ke ciki a matsayin abin damuwa.

Ya ce:

“An raba daliban zuwa kungiyoyi 25 a cikin dajin, inda ‘yan bindigan ke lura da kowane rukuni saboda tsoron hare-hare. An kewaya dani zuwa kowani sako don ganin yaran kuma na ga halin da suke ciki mai tayar da hankali.
“Lokacin da nake cikin daji tare da masu garkuwar an ba ni kyakkyawar kulawa, an ciyar dani naman shanu a duk tsawon zamana tare da su. Sun bani N11,000 a matsayin kudin mota; sun yi min kirki sosai.”

An gano yaran makarantar Islamiyyar Tegina a yankin Shiroro

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 67 a garkame, 'yan fashi sun sako mutane 4 da suka yi garkuwa da su a matsayin goron Sallah

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa an gano dalibai 136 da aka sace a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina, jihar Neja a yankin Lakpma na karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa uku daga cikin yaran sun mutu a hannun masu garkuwar.

Tafidan Allawa, shugaban kungiyar matasan kungiyoyin Allawa, Jibrin Allawa, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya yi kira da a dauki kwararan matakan ceto yaran, yana mai cewa yanzu sun zama kamar masu cutar yunwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel