Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake

Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake

- Daliban GSC Kagara sun bayyana irin azabar da suka sha a hannun 'yan bindiga da suka sace su

- Sun bayyana cewa wake kadai ake suke ci da kuma dankaren duka, ba sassautawa ko tausayawa

- Wani daga cikin daliban ya bayyana alhininsa da cewa ba lallai ya iya komawa makarantar ba

Dalibai, malamai da danginsu na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, jihar Neja da 'yan bindiga suka sace kwanaki 11 da suka gabata sun sun kubuta da sanyin safiyar jiya tare da labarin azabtarwa da wulakanci.

Amma suna farin ciki da cewa suna raye don bayar da labarai, ko da yake daya daga cikin daliban an garzaya da shi asibiti saboda abinda Gwamna Abubakar Sani Bello ya kira gajiyar da ta wuce kima.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin ciki da sakin su amma ya roki masu makarantun da su kara tsaro a cibiyoyin karantarwarsu domin dakile matsalar tsaro.

Amma da alama 'yan bindigar da ke ta'addanci yankin Kagara har yanzu ba su gama da al'umma ba, biyo bayan wani sabon hari da suka kai jiya.

KU KARANTA: Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo ba, haka aka sako 'yan GSC Kagara

Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake
Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Mazauna hudu aka kashe yayin da aka sace wasu 25 kuma aka yi awon gaba dasu.

An saki dalibai, malamai da danginsu na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara biyo bayan kammala tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar da 'yan ta'addan da karfe 1 na daren jiya.

Daga nan wadanda aka sace suka fara tafiya na tsawon awa takwas don fitowa daga kogon wadanda suka yi garkuwar da su.

Jami'an gwamnatin da aka tura domin kai su Minna sai suka fara bin diddigin su kafin su dauke su don tafiya zuwa babban birnin jihar.

Kai tsaye aka kaisu gidan Gwamnati inda gwamnan da kansa ya karbe su. Ya ce sun shiga mummunan hali a hannun wadanda suka sace su. Sakamakon haka, za a duba su a asibiti kafin hadasu da danginsu.

“Duk wadanda aka ceto din suna nan tare da mu. Sai dai, dayansu yana asibiti sakamakon gajiya. Na gode wa Allah da suka dawo nan tare da mu cikin lumana,” in ji gwamnan.

“Sun sami damar ba da labarin abin da suka fuskanta kuma abin takaici ne matuka. Sun kasance cikin tsananin azaba a hannun masu garkuwar. Muna lura da lafiyarsu da yanayinsu nan bada jimawa ba za su koma gida zuwa danginsu.”

Ya ce za a kula da yaran yadda ya kamata kuma nan ba da jimawa ba za a kai su ga danginsu bayan sun samu isassun kulawar lafiya.

Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake
Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Lokacin da suke ba da labarin yadda suka wahala, daliban sun ce an sanya su yin tafiya mai nisa kuma ana ba su wake ne kadai a matsayin abinci tsawon kwanakin da suka yi a dajin.

Wasu sun cika da alhini kuma sun fashe da kuka.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, Abubakar Sidi, dalibi dan ajin babbar sakandare na uku (SS3), ya ce 'yan bindigan sukan azabtar dasu kuma su ba su wake kadai su ci.

Babu isasshen ruwa, sau daya kawai ake basu ruwa su sha a rana.

"Sun wulakantamu ta duk yadda suka so," in ji shi.

“Su kan ba mu wake mu ci. Ruwansha bai da yawa. Wani lokaci a rana, muna shan ruwa sau daya kacal.

“Kai! Ba sauki. Ga kuma dankaren duka.”

Wani dalibi dan aji uku (SS3), Suleiman Lawal, ya ce ba a taba zaluntar sa kamar yadda 'yan bindiga suka zalunce shi ba.

“Mun sha wahala sosai. Ban taba fuskantar irin wannan halin a rayuwata ba. Munyi tafiya mai nisa. Bai kasance mana da sauki ba kwata-kwata," in ji shi.

Ya kuma bayyana bai da tabbatacin zai koma makaranta.

"Ba na tsammanin zan so in sake komawa waccar makarantar," in ji shi.

KU KARANTA: Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

A wani labarin, Dalibai da sauran wadanda aka suka sace daga GSC Kagara a Jihar Neja an sake su a safiyar ranar Asabar bayan amincewar jami'ai su saki mambobin 'yan bindigan su hudu, kamar yadda majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa Daily Trust ranar Lahadi.

Kungiyar 'yan bindigar sun kai hari a makarantar da ke cikin Karamar Hukumar Rafi a ranar 17 ga Fabrairu inda suka yi awon gaba da dalibai 27, da malamai 3, da ma'aikata 2 da ba sa koyarwa da iyalansu mutum 9.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.