Karin Bayani: Dan Majalisa Ya Tabbatar da Sace Daliban Yauri Na Jihar Kebbi

Karin Bayani: Dan Majalisa Ya Tabbatar da Sace Daliban Yauri Na Jihar Kebbi

  • Dan majalisar wakilai a majalisar tarayya ya gaskata faruwar harin da ya faru a yau a jihar Kebbi
  • Ya shaidawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja cewa, ya samu labarin daga majiya mai tushe
  • Ya koka ga gwamnatin tarayya kan cewa ta tallafa wajen tabbatar da an kubutar da daliban da malamansu

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ngaski/Shanga/Yauri ta Tarayya ta Jihar Kebbi a Majalisar Wakilai, Yusuf Tanko Sununu, ya tabbatar da sace dalibai da malaman Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri dake Jihar Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Sununu, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Majalisar Tarayya, ya ce har yanzu ba a gano adadin dalibai da malaman da aka sace ba.

KU KARANTA: Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: Dan Majalisa Ya Tabbar da Sace Daliban Yauri Na Jihar Kebbi
Taswirar Jihar Kebbi a Arewacin Najeriya | Hoto: allnigeriainfo.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

“Sun sami damar shiga ne bayan artabu mai karfi da suka yi da 'yan sanda wadanda ke gadin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri. Sun fasa hanya zuwa makarantar.
“Sun yi nasarar yin garkuwa da wasu malamai da kuma daliban da ba a san adadin su ba. Wasu daga cikin daliban da kuma jami'an tsaron a yanzu haka suna karbar kulawa a babban asibitin Yauri sakamakon raunukan da suka samu daga bindiga."

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su tashi tsaye don tabbatar da ceto daliban da malamansu da aka sace.

A baya jaridar Guardian ta ruwaito yadda wasu mutane dauke da muggan makamai suka kutsa cikin makarantar a ranar Alhamis.

Duk da ba tabbatar da adadin daliban da aka sace ba, an yi imanin cewa suna da yawa, kuma an harbi wasu daga cikinsu.

KU KARANTA: Baba Oyoyo: Muhimman Jawabai 11 da Shugaba Buhari Ya Yi a Ziyararsa Ta Borno

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi

A wani labarin, Labari da muke samu a yanzu ya nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai masu yawa daga Kwalejin Tarayya da ke garin Yauri a jihar Kebbi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa shaidar gani da ido sun ce maharan sun yi awon gaba da dalibai da dama sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

An tattaro cewa wani da abun ya faru a kan idonsa ya sanar da sashin labaran cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar sannan suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu inda suka zuba daliban sannan suka tafi da su.

An kuma ruwaito cewa maharan wadanda suka kai wa makarantar hari a kan babura sun fito ne daga dajin Rijau da ke makwabtaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel