Yadda harin Boko Haram, da sace yan matan makarantar Dapchi ya faru – Al’umman garin

Yadda harin Boko Haram, da sace yan matan makarantar Dapchi ya faru – Al’umman garin

Al’umman Dapchi, garin da aka kai hari a jihar Yobe a ranar Litinin, sun ce yan bindigan Boko Haram da suka kai hari garinsu basu da wani kudiri da ya wuce na sace dalibai mata na makarantar Girls Science and Technical College, Dapchi.

Iyaye, yan uwa da mazauna Dapchi, wani gari a jihar Yobe sun sanar da majiyarmu ta Premium Times cewa yan bindigan da suka kai hari garinsu sun kasance baki wadanda suka tursasa wasu mazauna garin nuna masu ciki da wajen garin.

“Sun kasance baki a garin, basu ma san inda makarantar ta GGSS take ba duk da cewar tana nan a bakin hanya ne a hanyar zuwa Gashua. Sannan a lokacin da suka gano inda makarantar ya ke, kai tsaye suka shiga suka kama yaranmu da dama sannan suka bar wajen ba tare da wani ya tunkare su ba, inji Muhammed cikin hawaye.

Abdullahi Jimuna, wani matashi day a bayyana kansa a matsayin tireda, yace har yanzu da dama daga cikinsu basu dawo daga alhinin da suka shigaba sakamakon wannan hari, wanda shine na farko da aka fara kaiwa garin.

Yadda harin Boko Haram, da sace yan matan makarantar Dapchi ya faru – Al’umman garin
Yadda harin Boko Haram, da sace yan matan makarantar Dapchi ya faru – Al’umman garin

Usman Na-Katarko wani manomi ya bayyana cewa yana da tabbacin yan matan sune musababbin shigowar yan ta’addan na Boko Haram yace hakan ya zamo bakon abu ga garin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari na so yan Najeriya suyi magana tukuna – Gwamna Bello

Wani mazaunin harin mai suna Garba Dapchi, yace da ace jami’an tsaro sun iso garin Dapchi sa’o’i bayan harin da sun yi nasarar kama masu garkuwan tare da ceto yan matan.

Al’umman garin dai da dama sun nuna bakin cikinsu da kuma alhini kan wannan lamari da yazo masu a bazata.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanatocin da ke wakiltar Jihar Yobe a Majalisar Dattawan Najeriya sun kaure da takkadama a tsakanin su game da sace wasu ‘Yan makaranta da aka yi kwanan nan a Garin Dapchi da ke Yobe. Sai da Shugaban Majalisa ya shiga tsakani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng