Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Karya Alkawari, Sun Turo Sabon Sako

Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Karya Alkawari, Sun Turo Sabon Sako

  • Ɓarayin da suka sace ɗalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna sun sake turo da sabuwar bukata
  • Rahoto ya nuna cewa sun sake neman a basu miliyan N50m bayan da farko sun karbi N100m
  • Shugaban Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, yace suna jiran yan bindigan su sako ragowar yaran a yanzun

Kaduna:- Bayan ana zargin sun karbi miliyan N100m tare da alkawarin sakin daliban Bethel Baptist dake hannunsu kashi-kashi, ɓarayin sun saɓa alkawarinsu.

Yan bindigan sun karya alkawarin da suka yi ne ta hanyar turo da sabuwar bukata ta naira miliyan N50m kafin su sako ragowar ɗalibai 83.

Barayin ɗaliban Bethel Baptist Kaduna sun sake aiko da muhimmin sako
Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Karya Alkawari, Sun Turo Sabon Sako Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin dagaske an biya miliyan N100m?

Wata majiya mai karfi ta shaidawa Vanguard cewa:

"Bayan iyayen yaran sun tattara miliyan N100m sun mikawa yan bindigan domin a sako 'ya'yansu, ɓarayin sun turo da dalibai 28 tare da alƙawarin sakin sauran kashi-kashi."
"Amma a yanzun sun sake neman a basu kuɗi miliyan N50m sannan su sako ragowar 83 dake hannunsu."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tawagar Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin Sace Mace Mai Juna Biyu a Sokoto

"Yanzun iyayen sun cire tsammani kuma sun shiga halin ruɗani da jin wannan labarin saboda sun siyar da komai da suka mallaka sun haɗa miliyan N100 da aka baiwa yan bindigan."

Shugabannin Baptist suna da wannan labarin?

Shugaban yan Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, yace sam ba shi da labarin sabuwar bukatar, domin basu sake ji daga yan bindigan ba.

"Har yanzun bamu ji daga gare su ba, muna jiran su sako mana sauran daliban dake hannunsu," inji shi.

Bamu biya kuɗin fansa ba

A baya shugaban Baptist na ƙasa, Israel Akanji, yace cocin su bata biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa domin a saki ɗaliban ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A cewarsa ba zai iya cewa komai ba game da abinda iyaye da masu fatan alkairi suka yi domin kubutar da yaran ba.

Akanji yace akwai yuwuwar wasu sun shiga lamarin ta wata hanya daban, kuma ba shi da iko amsa tambayar da take su yakamata ayi wa.

Kara karanta wannan

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

A wani labarin kuma Najeriya Ba Zata Koma Ruwa Ba, APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Atiku

A ranar Alhamis, bayan ganawa da Gwamna Wike na jihar Rivers, Atiku yace yan Najeriya Allah-Allah suke PDP ta dawo kan mulki a 2023.

Amma da yake martani kan maganar Atiku, Sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, John Akpanudoedehe, yace Najeriya ba zata koma ruwa ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel