Zaben Neja Ya Bar Baya da Kura, Matasa Sun Huce Fushinsu kan Gwamna Bago
- Ana ci gaba da jiran sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Neja da aka gudanar a ranar Asabar
- Sai dai, tun kafin sanar da sakamakon zaben, jam'iyyun adawa aun fara zargin tafka magudi don fifita jam'iyyar APC
- Hakazalika, wasu fusatattun matasa sun huce fushinsu kan Gwamna Umaru Bago a garinsa na Bida
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Jam’iyyun adawa da masu kada kuri’a sun yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a fadin jihar Neja.
Jam'iyyun adawan sun yi zargin magudi, hana jama’a kada kuri’a da murdiyar sakamakon zabe domin fifita jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce a kananan hukumomi 25 na jihar, ma’aikatan zabe da kayan aiki sun isa wuraren zabe ba a kan lokaci ba, yayin da wasu wurare ma ba a kai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me jam'iyyun adawa suka ce kan zaben Neja?
Jam’iyyun adawa sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC) da hada baki da APC don rage yawan masu kada kuri’a da kuma murde sakamakon zabe, zargin da hukumar ko jam’iyyar mai mulki ba su karyata ba har yanzu.
Duk da cewa ana ci gaba da tattara sakamako a lokacin da ake rubuta wannan rahoto, APC tana kan gaba da tazara mai nisa a yawancin kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli.
Sai dai zanga-zanga ta barke a Suleja, Wushishi, Lavun, da wasu kananan hukumomi, inda jama’a suka yin zargi murdiya da tsoratarwa daga jami’an tsaro.
Matasa sun farmaki ayarin Gwamna Bago
A halin da ake ciki, fusatattun matasa sun kai hari kan ayarin Gwamna Umar Bago a garinsa na Bida a ranar Lahadi.
Rahotan Daily Post ya ce matasan sun jefi motocin gwamnan da duwatsu, inda aka raunata wasu mutane ciki har da hadimin gwamna mai suna Abubakar Mustapha.
Majiyoyi sun bayyan cewa tashin hankalin ya biyo bayan wani shirin rabon kudi da ake zargin gwamnan ya shirya kafin zaben.
An ce Gwamna Bago ya raba kudi ga wasu 'yan kalilan daga cikin daruruwan mutane da suka taru a gidansa, abin da ya haifar da bacin rai da tarzoma.
Majiyoyi sun ce fusatattun matasan sun lalata hotunan gwamna da motocin yakin neman zabe.
Harin ya zo kwanaki biyu bayan hatsaniya da turmutsitsi a wani taro makamancin haka a Bida, inda wata yarinya ‘yar shekara 17 ta mutu, wasu kuma suka ji raunuka.
Rahotanni sun ce wasu mata sun gamu da fushin mazajensu bayan halartar taron ba tare da izini ba.

Source: Facebook
Ba a ji ta bakin gwamnati ba
Yunkurin jin ta bakin babban sakataren yada labaran gwamnan ya ci tura domin bai amsa kiran wayar da aka masa ba.
Hakazalika mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Jonathan Vatsa, bai dauki kiran wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Gwamna Bago ya bada hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bada hutu don gudanar da zaben kananan hukumomi.
Gwamna Bago ya ba da hutun ne domin bai wa jama’a damar halartar zaben kananan hukumomi da za a gudanar a fadin jihar.
Sanarwar da gwamnan ya fitar ta bayyana cewa kasuwanni, bankuna da ofisoshin gwamnati za su kasance a rufe a kwanakin hutun guda biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


