Barazanar Trump: Kwankwaso ya magantu kan lamarin, ya shawarci gwamnatin Tinubu

Barazanar Trump: Kwankwaso ya magantu kan lamarin, ya shawarci gwamnatin Tinubu

  • Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna damuwa kan maganganun Donald Trump game da Najeriya bayan zargin kisan Kiristoci
  • Jagoran Kwankwasiyya ya jaddada cewa Najeriya tana da ’yancin kai tare da kalubalen tsaro daban-daban
  • Ya ce matsalolin tsaro ba su bambanta addini ko kabila, yana rokon Amurka ta ba Najeriya fasahar yaki da ’yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana bayan barazanar kasar Amurka kan Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana damuwa kan maganganun Donald Trump game da Najeriya, bayan da ya ja layi kan kasar.

Kwankwaso ya tsoma baki kan barazanar Amurka kan Najeriya
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yayin jawabi ga manema labarai. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Jagoran siyasar Kwankwasiyya ya bayyana haka ne a yau Lahadi 2 ga watan Nuwambar 2025 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fusata da barazanar Amurka, ya ba Tinubu satar amsa

Wannan martani na tsohon gwamnan Kano ya biyo bayan barazana da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi a jiya Asabar 1 ga watan Nuwambar 2026.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin Amurka zuwa Najeriya idan gwamnati ta gaza daukar matakai.

Hakan na zuwa bayan Amurka ta nuna damuwa kan zargin yiwa Kiristoci kisan kiyashi wanda ya tayar da hankula.

Trump ya ce zai hana Najeriya tallafin ketare, ya kuma dauki mataki “mai tsauri cikin gaggawa” kan masu tayar da kayar baya.

Kwankwaso ya ba da shawara bayan barazanar Trump ga Najeriya
Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Twitter

Abin da Kwankwaso ya ce ga Amurka

Kwankwaso ya jaddada cewa Najeriya kasa ce mai ’yancin kai, kuma barazanar tsaro ba ta bambanta addini, kabila ko siyasa, yayin da ’yan ta’adda suke addabar jama’a.

Ya bukaci Amurka ta taimaka da fasahar zamani wajen yaki da matsalar tsaro, maimakon furucin da zai kara rarraba al’umma ko tayar da hankula.

A cikin rubutunsa, Kwankwaso ya ce:

"Na lura akwai damuwa game da maganar da Shugaba Donald Trump ke yi kan Najeriya, musamman bayan ya sanya ƙasarmu cikin jerin “ƙasashe masu damuwa ta musamman.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya

"Ya dace a jaddada cewa ƙasarmu ƙasa ce mai cikakken ‘yanci wacce al’ummarta ke fuskantar barazana daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
"Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin tsaron Najeriya da fasahohin zamani don magance waɗannan matsaloli, maimakon ta ɗauki matakan da za su ƙara rarrabuwa a ƙasarmu."

Shawarar Kwankwaso ga gwamantin Tinubu

Ya kuma shawarci gwamnati ta nada jakadu na musamman da kuma jakadu cikakku domin karfafa hulda da Amurka da kare muradun Najeriya a duniya.

A karshe, ya kira ’yan kasa da su kasance tsintsiya madaurinki daya a wannan lokaci, yana cewa lokaci ne na hadin kai inda ya yi addu'ar Allah ya albarkaci Najeriya.

"Haka kuma, ya dace gwamnatin Najeriya ta nada jakadu na musamman daga cikin manyan diplomasiyyar ƙasar domin tattaunawa da gwamnatin Amurka.
"Bugu da ƙari, akwai bukatar a nada jakadu na dindindin domin kare muradun Najeriya a matakin duniya.
"Ga ‘yan uwana ‘yan kasa, wannan lokaci ne da ya kamata mu fifita haɗin kai da kishin kasa fiye da rarrabuwar kai."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan

Lauya a Amurka ya saba da Trump kan barazana ga Najeriya, ya fadi ciwon da ke damunsa

Tinubu ya magantu kan barazanar Trump

Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi martani kan barazanar da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan kawo hari Najeriya.

Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa shugabannin kasashen biyu za su gana domin tattaunawa kan batun.

Daniel Bwala ya bayyana cewa dukkanin shugabannin biyu suna da manufa iri daya ta yaki da ta'addanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.