Wata Sabuwa: Lauyoyi Na Shirin Kawo Cikas ga Tabbatar da Nadin Shugaban INEC a Majalisa

Wata Sabuwa: Lauyoyi Na Shirin Kawo Cikas ga Tabbatar da Nadin Shugaban INEC a Majalisa

  • Bola Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)
  • Wata gamayyar kungiyar lauyoyi ta nuna rashin gamsuwarta kan nadin da Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya yi
  • Ta mika bukatarta gaban majalisar dattawa kan shirin tabbatar da Farfesa Amupitan a shugabancin hukumar INEC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wata gamayyar lauyoyi fiye da 1,000 da ke aiki karkashin kungiyar Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners (ALDRAP) ta yi kira majalisar dattawa.

Kungiyar ALDRAP ta bukaci majalisar dattawa ta ki amincewa da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

An bukaci majalisa ta ki tabbatar da Amupitan a shugabancin INEC
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan. Hoto: Joash Ojo Amupitan
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da kungiyar ta rubuta a ranar 10 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Da gaske sabon shugaban INEC na cikin lauyoyin Tinubu a zaben 2023? an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyi sun koka kan nadin Joash Amupitan

An aika wasikar wadda sakataren kungiyar, Jesse Williams Amuga, ya sanyawa hannu ga shugaban kwamitin zaɓe na majalisar dattawa, Sanata Simon Lalong.

Kungiyar ta zargi Farfesa Amupitan da rashin cancanta saboda rawar da ya taka a baya a matsayin lauyan jam’iyyar APC yayin da ake sauraron karar zaɓen shugaban kasa na 2023 a Kotun Koli.

Ta ce bai kamata majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Amupitan ba, sai dai ta sanar da shugaban kasa cewa bai cika ka’idodin da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

“Majalisar Dattawa ta riga ta kafa misali tun a 2021 lokacin da ta ki amincewa da nadin Lauretta Onochie saboda alakarta da jam’iyyar APC. Hakan ya zama ka’ida, kuma lamarin Farfesa Amupitan ya yi kama da irin na ta."

- Jesse Williams Amuga

Wace bukata aka nema a majalisar dattawa?

“Tun da ya riga ya yi aiki a matsayin babban lauya ga jam’iyyar APC, Farfesa Amupitan ba zai iya gudanar da aikinsa a matsayin shugaban INEC cikin gaskiya ba, musamman a zaɓen da ya shafi APC da sauran jam’iyyu."

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

- Jesse Williams Amuga

ALDRAP ta jaddada cewa Najeriya na da lauyoyi sama da 200,000 wadanda fiye da rabinsu ba su da alaka da kowace jam’iyyar siyasa, kuma za a iya zaɓar ɗaya daga cikinsu ba tare da an nuna son kai ba.

Lauyoyi sun bukaci majalisa ka da ta tabbatar da nadin Amupitan
Farfesa Joash Amupitan wanda Bola Tinubu ya nada a matsayin shugaban INEC. Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

Ƙungiyar ta gargadi majalisar dattawa cewa idan ta tabbatar da nadin Amupitan, za ta daukaka kara a kotu.

"Idan majalisar dattawa ta tabbatar da Farfesa Joash Amupitan, kungiyarmu ba za ta yi wasa ba wajen kai kara domin tilasta bin ka’idar rashin nuna bambanci wajen tabbatar da shugaban INEC."

- Jesse Williams Amuga

Sai dai bincike ya nuna cewa Farfesa Joash Amupitan bai da alaka da APC kuma bai cikin lauyoyin Bola Tinubu a shari'ar zaben 2023.

ADC ta aika da sako ga Amupitan

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi kira ga sabon shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan.

Kara karanta wannan

Amupitan: Abubuwan da 'yan Najeriya ke so sabon shugaban INEC ya yi

ADC ta bukaci sabon shugaban na INEC da ya zama mai amana ga 'yan Najeriya wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Ta bukaci ka da ya yarda ya zama dan amshin shatan gwamnati yayin jagorancin da zai yi a hukumar INEC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng