Muhimman Abubuwa 10 game da Wanda Ake Tunanin Tinubu Zai Nada Shugaban INEC
Abuja - Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun nuna cewa Bola Tinubu na dab da yanke hukunci kan wanda zai mika wa ragamar hukumar zabe (INEC).
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa Shugaba Tinubu na duba yiwuwar nada Farfesa Joash Amupitan, SAN, a matsayin sabon shugaban INEC na kasa.

Source: Twitter
Jaridar This Day ta tattaro cewa Tinubu ya karkata kan Farfesan, dan asalin jihar Kogi yayin da wa'adin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya kusa karewa.
A wannan rahoton, mun tattaro maku muhimman abubuwa 10 kan Farfesan kuma masanin doka, wanda ake tsammanin zai karbi ragamar hukumar zaben Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Farfesa Amupitan ya kai matsayin SAN
A watan Agusta, 2014 Farfesa Amupitan ya zama babban lauya a Najeriya wanda ya kai matsayin SAN.
Wannan ya sa ya shiga cikin manyan lauyoyi masana harkokin doka da suka yi fice wajen samun nasarori a kotu.
2. Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos
Tun daga ranar 25 ga Oktoba, 2022, Amupitan ke rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jami’a (Harkokin Gudanarwa) a Jami’ar Jos har zuwa yau.
Farfesan ya shafe shekaru da dama yana koyar da harkokin doka watau shari'a a jami'ar Jos, da ke karkashin gwamnatin tarayya.
3. An haife shi a Jihar Kogi
Amupitan ya fito ne daga Aiyetoro-Gbede a Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, wacce ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
An haife shi a watan Afrilu, 1967 a garin Aiyetoro-Gbede da ke jihar Kogi, yanzu ya kai shekaru 58 kenan a duniya.
4. Gwarzon dalibin karatun lauya a 1987
A lokacin karatun digirinsa na farko, Amupitan ya kasance kan gaba a ajinsa, inda ya lashe manyan lambobin yabo a karatun lauya a Jami’ar Jos.
Daga cikin karramawar da aka masa saboda kokarinsa akwai lambar yabo ta Richard Akinjide da lambar yabo da ake ba gwarzon dalibi ta Shugaban Jami'ar Jos.
5. Digiri uku a fannin shari'a
Bayan samun digirin farko LL.B (Hons) a 1987, Amupitan ya kammala BL a Makarantar Koyar da Lauyoyi ta Najeriya a 1988.
Sannan Amupitan ya sami LL.M a 1993 da digirin Ph. D a fannin doka a 2007, duka daga Jami’ar Jos.
6. Ya zama Farfesa a fannin doka a 2008
Amupitan ya shiga Jami’ar Jos a 1989 a matsayin karamin malami, kuma ya ci gaba da aiki har ya zama Farfesa a ranar 1 ga Oktoba, 2008.
Ya jagoranci daliban digiri na biyu da na uku masu yawa, kuma ya lashe lambar yabo ta Teslim Elias Award a 2014.
7. Kwarewa a doka da gudanarwa
Fannin da Amupitan ya gudanar da bincike ya shafi dokar kamfanoni, dokar Gudanarwar Kamfanoni da kuma Dokar Shaida.
Ya koyar da wadannan fannoni a matakin digiri na farko tun daga 1989 da kuma a matakin digiri na biyu tun daga 2006 har zuwa yanzu.

Source: UGC
8. Manyan mukaman da ya rike a fannin doka
Daga 2006 zuwa 2012, Amupitan ya rike mukamin Shugaban Sashen Koyar da Ilimin Doka a Jama’a (HOD).
Sannan kuma ya zama Shugaban Tsangayar Koyar da Aikin Lauyoyi a Jami'ar Jos. An sake zabensa a karo na biyu a wannan matsayi a 2012.
9. Gogewa mai zurfi a fannin doka da shugabanci
Amupitan ya taka rawa a shari’o’i daban-daban a kotunan Najeriya, ya kasance mamba a kwamitocin gudanarwa na kamfanoni.
Bugu da kari, ya bayar da gudunmawa a tsarin mulki ta hanyar kasancewa cikin Vision 2020 da Kwamitin Bincike kan Rikicin Garin Namu.
10. Rubuce-rubuce da shahara a duniya
Amupitan ya wallafa sama da makaloli 70. Ya yi aiki a matsayin mai tantancewa da mai kimantawa ga Jami'o'i irin su University of Fort Hare (Afirka ta Kudu), National Islamic University Malaysia, da wasu jami’o’in Najeriya.
Haka kuma, Farfesa Amupitan shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami'ar Joseph Ayo Babalola.

Kara karanta wannan
"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027
Kotu ta umarci a kama shugaban INEC
A wani labarin, kum ji cewa Babbar Kotun Tarayya mai zama a Osogbo, jihar Osun ta zargi shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da raina umarninta.
Kotun ta bai wa Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, umarnin cafke Yakubu cikin mako daya idan ya gaza aiwatar da umarninta.
Mai shari’a Funmilola Demi- Ajayi, ce ta ba da umarnin yayin yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar AA da hukumar INEC kan zaben shugabannin jihohi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


