An Yi Rashi a Najeriya: Tsohon Minista kuma Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Rasu

An Yi Rashi a Najeriya: Tsohon Minista kuma Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Rasu

  • Sanata Solomon Ewuga, tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, kuma tsohon ministan Abuja ya rasu yana da shekara 70
  • Marigayin ya kasance jagoran siyasa, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen kafa jihar Nasarawa a Oktobar 1996
  • Mutuwar Sanata Ewuga ta girgiza mutane, musamman a Nasarawa, inda aka yi kira ga gwamnati ta ba da hutu don girmama shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Al’ummar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya sun shiga alhini bayan rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Sanata Solomon Ewuga.

Sanata Solomon Ewuga, ya rasu ne a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025 bayan dogon lokaci yana hidimtawa al'umma.

Tsohon ministan Abuja, kuma tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, Sanata Ewuga ya rasu
Hoton Sanata Sanata Ewuga, tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa. Hoto: @kabiruturakisan
Source: Twitter

Tsohon ministan Abuja, Ewuga ya rasu

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, Sanata Ewuga, wanda ya yi bikin karin shekara a ranar 19 ga Yuni, 2025 ya rasu yana da shekaru 70.

Kara karanta wannan

Zargin N3bn: Alkali ya fara fusata, an shekara 10 ana shari'ar tsohon gwamna da EFCC

Sanata Solomon Ewuga ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamna Abdullahi Adamu, sannan ya wakilci Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya ta bakwai.

Haka kuma ya taba rike mukamin karamin ministan babban birnin tarayya (FCT) Abuja. A Disambar 2023, ya koma APC daga jam'iyyar PDP, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Gudummuwa ga al’umma da abin da ake cewa

Sanata Ewuga ya kasance ginshiki wajen ƙirƙirar jihar Nasarawa, kana gidansa a Alushi ya zama cibiyar taro ga ‘yan siyasa da al’umma.

Babban lauya kuma ɗan fafutukar kare hakkin bil’adama, Chidi Anselm Odinkalu, ya yi jimamin mutuwarsa a shafinsa na X, yana mai cewa:

“Sanata Solomon Ewuga, aboki, ɗan uwa, mai gaskiya, yanzu ka koma ga mahaliccinka. Mun gode da irin jajircewar da ka nuna a rayuwarka!”

Wasu ‘yan ƙasa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta ayyana hutun biki don girmama shi, yayin da wasu suka bayyana shi a matsayin jagora mai sauƙin kai a Nasarawa.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

Marigayin ya fara karatun digiri a ilimin siyasa a jami’ar Ibadan tsakanin 1974-1977, kamar yadda bayanansa na Linkedin suka nuna.

Daga bisani ya yi karatun aikin jarida a jami’ar Stockholm (1980-1981), sannan ya kammala digirin lauya a jami’ar Jos (1984-1987), da makarantar koyon lauya ta Najeriya (1987-1988).

An yi kira ga gwamnatin Nasarawa ta ba da hutu don girmama Sanata Ewuga da ya rasu.
Taswirar jihar Nasarawa da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jimami da addu’o’in al’umma

Masu jimami, sun bayyana cewa mutuwar Sanata Ewuga babban rashi ne ga Nasarawa da Najeriya baki ɗaya.

Samuel Joel Ahmed:

"Don Allah ko gwamnatin jiha za ta ba da hutun kwana daya, domin girmama wannan babban gwarzo kuma jakadan zaman lafiya. Ubangiji ya jikanka, Sanata Ewuga.
"Wani abun burgewa game da shi shi ne, ma damar kuka hadu sau daya, to ka tabbata zai kira sunanka a haduwarku ta gaba. Lallai ba za a iya mantawa da shi ba."

Mansur Ibrahim:

"In har ana maganar siyasar Nasarawa, to dole sai an saka da sunan Ewuga a ciki. Za mu yi kewar jajurtaccen mutum mai nagarta."

Ewuga ya ja kunnen Jonathan kan takara

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Solomon Ewuga (marigayi) ya taba yin kira ga Goodluck Jonathan da ya yi watsi da masu neman ya sake yin takara a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da hadimin gwamnan Nasarawa

Tsohon ministan na Abuja, Sanata Ewuga ya shaidawa Jonathan cewa sake fitowa neman kujerar shugaban kasa zai bata masa suna da kimarsa ne kurum.

A hirar da ya yi, Sanata Ewuga ya kuma ba jam’iyyar hamayya ta PDP shawara ta gyara duk wasu kura-kuran da tayi a baya, idan ta na so al’umma su sake zabenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com