Jam’iyyar APC na shirin dauke wani babban ‘Dan siyasan PDP a Nasarawa

Jam’iyyar APC na shirin dauke wani babban ‘Dan siyasan PDP a Nasarawa

Wani tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja, kuma babban jigo a jam’iyyar PDP a Arewacin jihar Nasarawa, Solomon Ewuga, yana daf da tserewa daga PDP ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Jam’iyyar APC na shirin dauke wani babban ‘Dan siyasan PDP a Nasarawa

Gwamnan Nasarawa yana neman jawo Sanata Ewuga zuwa APC
Source: Twitter

A yayin da ake shirin zaben 2019, Sanata Solomon Ewuga da dinbin mabiyan sa sun fara tunanin sauya-sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC a jihar Nasarawa. Ewuga ya kyankyashi wannan shiri ne bayan ya rasa takarar gwamna a PDP.

Solomon Ewuga ya fara lissafin komawa APC ne tun bayan da gwamna mai shirin barin-gado, Umaru Tanko Al-Makura, ya nada sa a matsayin shugaban tawagar safarar kiristocin jihar zuwa kasar Jerusalem domin su sauke farali.

KU KARANTA: Atiku Abubakar zai doke Buhari ragas a zaben 2019 - babban Lauya

Sanata Ewuga ya jinjinawa gwamna Al-Makura bayan an nada sa wannan mukami, wannan ya sa wasu ke ganin cewa gwamnatin APC da ke mulki a jihar ta jawo tsohon Sanatan jikin ta ne domin ta samu damar yi wa PDP illa a 2019.

Tsohon ‘Dan takarar gwamnan ya na da jama’a sosai a jihar Nasarawa musamman kiristocin jihar. Wadanda su ka lakanci siyasar Nasarawa sun ce komawar su APC zai yi wa PDP babbar nakasa a zaben da za a gudanar a shekarar badi.

Ewuga yana cikin wadanda su ka taimakawa gwamna Tanko Al-Makura ya doke Marigayi Aliyu Akwe Doma a 2011. Kwanaki ne dai PDP ta hana Ewuga takara, inda ta tsaida David Ombugadu a matsayin wanda zai rike mata tuta a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel