'Yan Takara 10 na Kujerar gwamnatin Jihar Nasarawa sun amince da dan Takara daya
Akalla 'yan takarar gwamnan jihar Nasarawa 10 sun yanke shawarar sanya bambance bambancen su a gefe guda domin tsayar da dan takara daya a domin mara ma sa baya a matsayin gwamnan jihar a zaben 2019.
Jiga-jigan masu neman takara a jam'iyyun da suka hadar da APC, PDP, APGA da kuma RP sun halarci taron da aka gudanar karkashin yankin Eggon dake mazabar Arewacin Jihar da aka kayyade ma ta kujerar gwamnan jihar a wannan lokaci.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, 'yan takarar sun kulla wannan yarjejeniya ta aminci yayin taron cibiyar Dattawan Eggon da aka gudanar a fadar Sarkin Eggon.
'Yan takarar da suka halarci taron sun hadar da; Mista Labaran Maku (APGA), Mr. Solomon Ewuga (PDP), Mr. Godiya Akwashiki (APC), Patricial Akwashiki (PDP), James Angbazu (APC), Adamu Adogi (APC), Inusa Muhammad (APC), Danladi Envuluanza (APC), Dauda Kigbu (APC), da Mista Mathew Ombugaku (RP).
KARANTA KUMA: Hayaƙin Janareta ya kar wata Uwa da 'Ya'yan ta 5 a jihar Edo
Sauran 'yan takarar na yankin Eggon da basu halarci taron ba kuma ba tare da aiko wakili ko uzuri rashin halarcin su ba sun hadar da; Mr. Zakari Idde (APC), Mista David Ombugadu (PDP) da kuma Mista Reuben Anjugu (APC)
Da yake jawabi bayan taron, Shugaban Kungiyar dattawa Eggon Mista Jato Anga ya bayyana cewa, 'yan takarar sun hada kawunan su ne da manufa wajen amfani da damar su a zaben 2019 ta tabbatar da dan takarar Eggon ya zamto gwamnan jihar Nasarawa na gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng